Serge Aurier zai shafe wata biyu a kurkuku

Asalin hoton, AFP
An wallafa
An yanke wa dan wasan kwallon kafa na kasar Ivory Coast, Serge Aurier, wanda ya ke buga wa kulob din Paris St-Germain wasa, hukuncin zama a gidan yari.
Serge Aurier dai zai shafe watanni biyu a gidan kaso bayan da ya yi wa wani dan sanda gula.
An kuma ci tarar dan wasan $674 a kan lamarin wanda ya faru a wani wurin holewa a Paris a watan Mayu.
A halin yanzu dai an saki Serge Aurier, har sai bayan daukaka kara, wanda hakan ke nufin zai iya buga wa Paris St-Germain din wasa a gasar Champions League a ranar Laraba.
An dai dakatar da dan wasan mai shekaru 23 a farkon wannan shekarar bayan ya yi kalaman batanci a kan kocin kulob din na PSG.








