Shugabannin Kannywood sun kori Rahama Sadau

Hadaddiyar kungiyar masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan Hausa, wato MOPPAN, ta kori shahararriyar 'yar wasan kwaikwayon nan Rahama Sadau.
Wannan mataki dai ya biyo bayan wani taro ne da kungiyar ta yi da yammacin ranar Lahadi.
A wata sanarwa da sakatarenta, Salisu Mohammed (Officer), ya sanyawa hannu, ta ce ta dauki wannan mataki ne da yawun dukkan kungiyoyin masu harkar shirya fina-finai, wadanda ke da wakilci a kungiyar.
Kungiyar ta ce 'yar wasan ta yi karan-tsaye ga ka'idojin kyawawan dabi'un da Kannywood ta ginu a kansu, lamarin da ta ce shugabannin harkar ba za su lamunce da shi ba.
Sanarwar ta kara da cewa an sallami 'yar wasan ne saboda fitowar da ta yi a wani faifan bidiyo na waka, inda take rungumar wani mawaki mai suna Classiq.
Kungiyar ta kuma ce an kafa wani kwamiti da zai saurari korafe-korafe da martani game da wannan mataki, musamman daga furodusoshin (masu shirya fina-finan) da a yanzu haka take taka rawa a fina-finansu.
Faifan bidiyon da Rahama ta fito a ciki dai ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu sha'awar fiana-finan Hausa.
Har yanzu dai jarumar, wacce ke kasar Indiya, ba ta ce komai ba a kan matakin.












