Kamaru: Jirgin kasa ya kashe mutane da dama

Asalin hoton, Camer 24
An wallafa
Akalla mutane goma ne suka rasa rayukansu bayan da wani jirgin kasa ya yi hadari a Kamaru.
Kamfanin kula da zirga-zirgar jiragen sama na kasar ya ce hadarin ya faru ne a tsakanin biranen Yaounde da Douala.
Wakilin BBC a kasar ya ce mutane da dama sun samu raunuka a hadarin.
Ya ce motocin daukar marasa lafiya sun wurin da lamarin ya faru a Eseka - wanda ke tsakanin Yaounde da Douala.
Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mutane suka makale a tsakankanun taragun jiragen.
Rahotanni sun ce an kara yawan taragun jiragen saboda an rufe babbar hanyar da ta hada garuruwan biyu sakamakon rugujewar wata gada.








