Zola ya zama kocin Birmingham

Zola tsohon dan wasan Chelsea da Italiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, West Ham da Cagliari da Al-Arabi ta Qatar duk sun sallami Gianfranco Zola
An wallafa

Kungiyar Birmingham City ta gasar Championshiop ta kasa da Premier, ta nada Gianfranco Zola ya maye gurbin Gary Rowett wanda ta kora a matsayin kocinta.

Zola mai shekara 50, wanda tsohon dan wasan Chelsea ne da Italiya, ya kulla yarjejeniyar shekara biyu da rabi ne da kungiyar.

A ranar Laraba ne kungiyar ta Birmingham wadda ke matsayin ta bakwai a teburin gasar ta 'yan dagaji, ta kori Rowett bayan sama da shekara biyu yana mata kociya.

Wasan farko da Zola zai jagoranci kungiyar shi ne na ranar Asabar a gida da ta daya a teburinsu Brighton.

Aikin koci na karshe da Zola ya yi a Qatar ne da kungiyar Al-Arabi wadda ta kore shi a watan Yuni, bayan shekara daya kawai .

Kafin wannan tsohon dan wasan na Italiya ya yi kocin West Ham, da kungiyar Cagilari ta Serie A .