Kalli hotunan maniyatan da suka je aikin hajji da keke

An wallafa

Kalli hotunan maniyatan da suka je Madinah da keke bayan sun yi tafiyar kilomita 3,000 daga London.

Hajj Ride

Asalin hoton, Facebook/HajjRide

Bayanan hoto, Maniyatan sun tashi zuwa aikin hajji ne a kan kekuna daga Landan ne domin su taimaka wajen tara wa wadan da yakin Siriya ya raba da gidajensu kudi don sayen magunguna.
Hajj Ride

Asalin hoton, Facebook/HajjRide

Bayanan hoto, Maniyyatan suna neman a tara fam miliyan daya saboda 'yan gudun hijirar Siriya.
Hajj Ride

Asalin hoton, Facebook/HajjRide

Bayanan hoto, Maniyatan sun dauki hoto a gaban masallacin gabashin Landan kafin su tashi
Hajj Ride

Asalin hoton, Facebook/HajjRide

Bayanan hoto, A wasu lokutan maniyyatan sun daga kekunansu kamar yadda suka yi da suka isa Girka.
Hajj Ride

Asalin hoton, Facebook/HajjRide

Bayanan hoto, Maniyyatan sun tsaya a Faransa a kan hanyarsu ta zuwa aikin hajji.
Hajj Ride

Asalin hoton, Facebook/HajjRide

Bayanan hoto, Tafiyarsu hajji ta keke ta ja hankalin mutane a sassan duniya inda aka yi ta amfani da maudu'in #HajjRide.
Hajj Ride

Asalin hoton, Facebook/HajjRide

Bayanan hoto, Maniyatan sun ratsa kasashe daban-daban da teku-teku a kan hanyarsu ta zuwa Madinah. Da farko dai sun so ratsawa ne ta kasashen Turkiyya da Syria da Jordan, amma saboda matsalar tsaro sai suka tafi da jirgin ruwa daga Girka zuwa Masar, inda daga can kuma suka shiga jirgin sama da ya kai su Jiddah.
Hajj Ride

Asalin hoton, Facebook/HajjRide

Bayanan hoto, Tafiyar ta faro ne daga yankin Gabashin London inda suka tuka kekunansu zuwa New Haven, sai suka hau karamin jirgin ruwa zuwa Dieppe na Faransa.