Kalli yadda Robert Mugabe ya sha gwagwarmayar siyasa

Bayanan bidiyo, Kalli yadda Mugabe ya sha gwagwarmaya
An wallafa

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya yi murabus daga kan mulki, kamar yadda Kakakin Majalisar Dokokin kasar Jacob Mudenda ya sanar.

An yi masa daurin talala bayan sojoji sun kwace iko a makon jiya, sannan aka rinka zanga-zangar nuna adawa da mulkinsa.

Mun yi nazari kan rayuwar shugaban, mai shekara 93, wanda ya shafe shekara 37 a kan karagar mulki.