Kim Jong-un zai tattauna da Moon Jae-in a Koriya ta Kudu

Kim Jong-un zai taka ne da kafarsa ya tsallaka wani layi da sojoji suka shata daya raba tsakanin kasashen biyu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kim Jong-un zai taka ne da kafarsa ya tsallaka wani layi da sojoji suka shata daya raba tsakanin kasashen biyu
An wallafa

A yankin Koriya ana shirye-shiryen fara wani taro inda Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un zai tafi da tawagar manyan jami'an kasar cikin su har da kanwar sa zuwa taron da zai yi da shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in.

Daga cikin muhimman batutuwan da taron zai duba a wani wuri mai matukar tsaro da ke kan iyakar kasashen sun hada da batun jingine ayyukan makaman nukiliya a yankin.

Shi dai Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un zai taka ne da kafarsa ya tsallaka wani layi da sojoji suka shata daya raba tsakanin kasashen biyu.

Hakan zai sa shi kasancewa shugaban Koriya ta Arewa na farko da zai sa kafarsa a Koriya ta Kudu tun bayan da aka kammala yakin Koriya.

Daga nan ne shugabannin biyu za su jera zuwa tattaunarwar da aka yi wa lakabi da " tattaunarwa zaman lafiya".

Mr Kim zai zagaya don ganin faretin girmamawa daga sojojin Koriya ta Kudu za su yi, inda daga bisani kuma sai shugabannin biyu su dasa itatuwa.

Za dai a rubuta jikin wani allo kusa da inda suka shuka itatuwan kalmomi da ke cewa: "Anan muka shuka zaman lafiya da ci gaba"- kuma daga nan ne sai shugabannin biyu su ci abincin dare tare.

Kawo yanzu dai ba'a san takamammen yadda bangarorin biyu zasu cimma yarjejeniya ba kan shirin makaman nukiliyar Koriya ta Arewa.

Sai dai ana kallon wannan taro a matsayin muhimmin ci gaba da aka samu bayan shafe shekaru ana zaman marina tsakanin bangarorin biyu.

Kazalika, taron zai share fagen yiwuwar ganawa tsakanin Kim Jong-un da shugaba Donald Trump a karshen watan Mayu ko kuma farkon watan Yuni.