An samu karin reshen kungiyar al-Qae'da a Mali

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Amirka ta sanya sunan wata kungiya a jerin ta 'yan ta'adda, bayan ta kira kan ta reshen al-Qa'eda a kasar Mali.
Gamayyar kungiyoyi uku masu dauke d makamai su ne suka samar da kungiyar Jama'atu Nusrat al-Islam wal-Muslimin, ta kuma yi ikirarin kai hare-haren da akai asarar rayuka a kasar a watan Mayun bara.
Ayyana ta a jerin 'yan ta'adda na nufin Amirka za ta dauki mataki kan ta kamar sauran kungiyoyin 'yan ta'adda irin IS.
Sannan haramcin mu'amala da ita ya rataya a wuyan duk Amirkawa kam daga musayar kudade da sauransu.








