Ana dakon sakamakon zaben jihar Osun

INEC
Bayanan hoto, Mutum uku 'yn snd suka kama da makudan kudade da suke kokarin sayan kuri'a a hannun masu zaben
An wallafa

Al'umar jihar Osun da ke kudu ma so yammacin Nigeria, na dakon sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a ranar asabar.

Rundunar 'yan sanda a Najeriya, ta ce ta kama wasu mutane da ke shirin satar akwatunan zabe a jihar Osun.

Kama mutanen dai ya zo a daidai lokacin da dubun wasu mutum uku ta cika a yayin da su ke sayan kuri'u a jihar.

Babban jmi'in hulda da jam' na sifeto jnr na 'yan sandan Niajeriya, Bala Ibrahim ya shaidawa BBC cewa an kama kudi sama da dubu dari shida a hannun mutum na farko, da ke kokarin sayan kuri'aa hannun msu zabe.

Ya yin da aka samu sama da naira dubu dari a hannun mutum na biyu, kuma tuni aka ta keyarsu zuwa ofishin 'yan sanda dan fara gudanar da bincike.

'Yan takara arba'in da takwas da su ka fito daga jam'iyyu arba'in da takwas ne za su fafata domin neman wannan kujera.