Gwamnatin Masar ta far wa gidajen yada labarai

President al sisi of Egypt

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

A Masar, hukumomin kasar sun kai wani samame a ofishin wata jarida mai zaman kanta, kwanaki bayan da suka kwace kaddarori mallakan jaridar.

Gamal Sultan, wanda shi ne editan jaridar Al-Mesryoon daily, ya bayyana cewa hukumomin na tuhumar su da cewa suna da alaka da haramtacciyar kungiyar 'yan uwa Musulmi, kuma suna mara masu baya.

Editan jaridar ya sanar da aukuwar wannan samamen ne kai tsaye ta hanyar wani sakon Twitter da ya aika, yana cewa jami'an tsaro suna tsare ma'aikatan jaridar da editocinta, kuma sun kwace dukkan kayan aikin da suka taras.

Dama gwamnatin Masar ta dode shafin jaridar na intanet tun bara, tare da wasu shafukan intanet fiye da 500, wadanda yawansu na jarida ne.

A ranar 11 ga watan nan, gwamnatin kasar ta bayyana cewa ta kwace kaddarorin wasu mutum 1,589, da kamfanoni 118, da kungiyoyin fararen hula 1,133, da makarantu 104 da asibitoci 69 da kuma shafukan intanet 33, har da wata tashar talabijin ta tauraron dan Adam.

A watan Afrilu ma an kai irin wannan hare-haren a kan ofishin wata jarida mai zaman kanta, Masr al-Arabia, inda aka tsare editanta, aka kuma tuhume shi da shiga kungiyar 'yan ta'adda.

Gwamnatin Masar ta ayyana kungiyar 'yan uwa Musulmi a matsayin kungiyar ta'addanci tun 2013, bayan da sojojin kasar suka hambarar da gwamnatin shugaban kasar na da Mohamed Morsi.