APC ta sake dage zaben Lagos, Adamawa da Enugu

APC
Bayanan hoto, Shugaban jam'iyyar APC Adams Oshimole
An wallafa

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sake dage zaben fitar da gwani a jihohin Lagos da Adamawa da Enugu.

A jiya lahadi aka sanar da dage zaben na jihar Lagos, a daidai lokacin da wasu jihohin kasar suke gudanar da zaben.

Cacar-baki da musayar zafafan kalamai tsakanin gwamnan Lagos Akunwumi Ambode da dan takarar gwamna Alhaji Babajide Sam Olu sun ci gaba da daukar hankalin jama'a.

APC ta tsayar da ranar Talata 2 ga Oktoba a matsayin ranar da za a yi zaben fitar da gwanin a jihar.

Jam'iyyar APC ta kuma dage zaben jihohin Adamawa da Enugu, tare da sauya shi zuwa tsarin 'yar tinke sabanin bin tsarin wakilai kamar yadda aka shirya tun a farko.

An tsaida ranar Alhamis 4 ga watan Oktoba dan gudanar da zaben a jihohin Adamawa da Enugu.