Uganda za ta haramta kamfanonin cacar wasanni a kasar

Caca ta zama sana'a ga matasan kasar da yawa
Bayanan hoto, Caca ta zama sana'a ga matasan kasar da yawa
An wallafa

Kasar Uganda ta bayyana cewa ba za ta sake bai wa kamfanonin caca lasisi a kasar ba.

Wannan wani yunkuri ne da kasar ke yi domin hana caca a kasar kamar yadda jaridar Daily Monitor ta ruwaito ministan tattalin arzikin kasar, David Bahati, yana cewa.

"Mun samu umurni ne daga shugaban kasa Yoweri Museveni da mu dakatar da cacar wasanni da kamfanonin caca.

Shugaban kasa ya bawa hukumar dake kula da su wannan umurni," a cewar Mr Bahati.

Ministan ya bayyana cewa shugaban kasar ya bada wannan umurni ne sabado illar da caca ke haifarwa kanana yara a kasar.

Shugaban kasa Yoweri Museveni ne ya bada umurnin

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaban kasa Yoweri Museveni ne ya bada umurnin

Cacar wasannin kwallon kafa babbar sana'a ce a kasar kuma tana ci gaba da habbaka.

Matasa da yawa marassa aikin yi a kasar sun shiga harkar caca ne inda suke fatan gina rayuwarsu, kamar yadda BBC ta ruwaito a 2017.

"Daga yanzu, babu wani sabon kamfanin da za a yi wa rajista. Wadanda aka yi wa rajista ba za a sake ba su lasisi ba idan wa'adin sake lasisi yayi."

Mr Bahati ya fada wa mutane a cikin cocin Rugarama dake garin Kabale.

Ya kuma bayyana cewa Fastocin coci dake adawa da cacar na iya yin murna a yanzu domin addu'arsu an karbe ta.