Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Macedonia na daf da shiga kungiyar NATO
Kasar Macedonia ta kara matsawa kusa da zama mambar kungiyar tsaro ta NATO da kuma sauya sunanta zuwa Macedonia ta Arewa.
Wannan ya biyo bayan bikin rattaba matakin ne a birnin Brussels inda mambobin kungiyar NATO su 29 suka sanya hannun shigar da ita cikin kungiyar.
Da zarar majalisar kasar Girka ta amince da matakin, Macedonia za ta dauki matakin kammala sauyin sunan nata.
Ana ta annashuwa wajen bikin sanya hannu, inda jakadan kasar Girka a kungiyar tsaro ta NATO ya wakilci kasarsa.
Wannan matakin ya kasance mai muhimmanci - domin ana sa ran zai kawo zaman lafiya mai dorewa tsakanin Girka da makwabciyarta da ke arewa.
Abin da ya rage shi ne majalisar kasar Girka ta amince da wannan yarjejeniyar da zai ba kasar arewacin Macedonia damar zama mambar NATO a matsayin kasa ta 30.
Ana sa ran aiwatar da matakin ranar Juma'a, wanda ke nufin sauyin sunan ya zama doka ke nan.
Babban sakataren NATO Jens Stoltenberg ya yaba wa abin da ya kira karfin guiwar da shugabannin kasashen biyu suka nuna.
Shi kuma shugaban kasar Macedonia, Nikola Dimitrov ya ce shigar kasarsa cikin kungiyar ta NATO zai tabbatar da zaman lafiya a yankin Balkans.