May Day: Yau ce ranar ma'aikata ta duniya

Bayanan sautiYau ce Ranar Ma'aikata ta Duniya
An wallafa

An kebe ranar 1 ga watan Mayu ne duk shekara matsayin ranar ma'aikata a fadin duniya, amma a Najeriya daya daga cikin kungiyoyin kwadago na kokawa.

Wata kungiyar kwadago ta kasar wato ULC ta ce suna murnar wannan rana, amma ba ta kai zuci ba saboda matsalolin rayuwa da ma'aikatan ke ciki.

Comrade Nasiru Kabiru Sakataren Tsare-tsare na kungiyar ta ULC a Najeriya ne ya shaida wa BBC damuwarsu.

Sai ku latsa hoto na sama domin sauraren yadda hirar ta kasance da wakilinmu Abdou Halilou.

A yawancin sassan na duniya ana kiran ranar da sunanta na Turancin Ingilishi wato May Day.