Kun san makomar Sanchez, Neymar da Monreal?

Neymar
An wallafa

Manchester United za ta jira sakamakon gwajin lafiyar dan wasan gabanta dan kasar Faransa, Anthony Martial mai shekaru 23, kafin ta yarda ta bayar da aron Alexis Sanchez zuwa kungiyar Inter Milan. (guardian)

PSG ta ce ba za ta sayar wa da Real Madrid dan wasanta ba Neymar mai shekaru 27, har sai ta yarda ta sanya dan wasan gabanta dan asalin Brazil, Vinicius Jr a cikin cinikin. (AS)

Su kuwa daraktocin kungiyar Barcelona sun taru domin tattaunawa kan cinikin tsohon dan wasanta, Neymar Jr. (marca)

Inter milan na kokarin komawa kan tsohon dan wasan Manchester City, Wilfried Bony, dan wasan mai shekaru 30 dan kasar Ivory Coast, a yanzu dai ba shi da kulob bayan kwantaraginsa ya kare da kungiyar Swansea a wannan kakar wasannin. (goal.com)

Tsohon dan wasan kasar Serbia Nemanja Matic mai shekaru 31 na bukatar tattaunawa da kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer bayan rashin nasarar da kungiyar ta yi a Old Trafford a karon farko. (mirror)

Arsenal ta ce a shirye take ta kyale dan wasan kasar Spaniya Nacho Monreal ya tafi Real Sociedad a wannan satin matukar dan wasan mai shekaru 33 ya bukaci hakan. (sun)

Wakilan dan wasan Denmark Christian Eriksen sun ki yarda da tayin kudin da Tottenham ta yi wa dan wasan na biyansa fam 200,000 duk mako yayin da kwantaraginsa ke neman karewa a kakar wasanni ta bana, yanzu dai dan wasan na daf da komawa Spain da taka leda. (mirror)

A iya cewa Erikson ya saduda ya zauna a Tottenham na wani dan lokaci, kasancewa ya kasa cika burinsa na komawa Real Madrid ko Barcelona a wannan kakar wasannin. (mail)

Dan wasan gaban Chelsea, Tammy Abraham na daf da rattaba hannu kan wata yarjejeniya da za ta sa a biya shi kudi ninkin abin da fam 50,000 a ko wanne sati. (telegraph)

Jami'an Inter Milan da na Juventus sun cimma yarjejeniyar wata musaya tsakanin yan wasan Argentina Mauro Icardi mai shekaru 26, da kuma Paulo Dybala mai shekaru 25. (gazzetta dello Sport - in Italian)