Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikici na neman barkewa tsakanin Isra'ila da Hezbollah,
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta harba rokoki kimanin 100 a kan yankunan kungiyar mayakan Hezbollah a kudancin Lebanon, a matsayin martani na wasu makaman roka da 'yan kungiyar ta Shi'a suka harba cikin arewacin Isra'ila ranar Asabar da yamma.
Hezbollah ta ce mayakanta sun lalata wata motar sojoji, yayin da Isra'ilar ta ce ba wanda ya jikkata a sanadiyyar hare-haren kungiyar ta Lebanon.
Kamar yadda rundunar sojin kasa ta Isra'ilar ta sanar, ta ce, an harba wasu 'yan makaman roka masu tarwatsa igwa-igwa kan wani sansanin soji da kuma kan wasu motocin yaki nata, daga kasar Lebanon.
Kasar ta ce a saboda haka ne ita ma ta mayar da martani da makamai masu linzami da jiragen yaki masu saukar ungulu, inda ta harba makaman atilari kusan 100, zuwa sansanonin mayakan Hezbollah a cikin Lebanon.
Duk da cewa Hezbollah ta yi ikirarin cewa ta tarwatsa wata igwa ta sojin Israila, da kashe sojoji da dama, Firaministan Isra'ilar Benjamin Netanyahu, ya ce sam-sam ba wani da ya jikkata daga bangarensu, hasali ma ko kwarzane ba wanda ya yi, in ji shi.
Daman an yi tsammanin kungiyar Hezbollah za ta mayar da martani bayan wasu hare-haren jirage marassa matuka da Isra'ila ta kai a cikin Beirut, babban birnin kasar Lebanon, mako daya da ya wuce.
Duk da cewa kasar ta Yahudu ba ta fito fili ta dauki alhakin kai hare-haren ba, amma ta gargadi Hezbollah cewa, ba za ta bari kungiyar ta mayaka 'yan Shi'a ta kirkiro makamai masu linzami na yankan-shakku ba a Lebanon tare da taimakon babbar mai mara mata baya Iran ba.
Wani mai magana da yawun rundunar sojin kasa ta Isra'ila ya ce a yanzu dai an kawo karshen wannan dauki-ba-dadi, kamar yadda ya ce. Amma kuma an ruwaito Firaministan Isra'ilar Benjamin Netanyahu ya ce kasarsa a shirye take da duk wata barazana.
Ba a dai samu wani babban rikici ba tsakanin Isra'ila da Hezbollah tun shekara ta 2006, lokacin da aka hallaka mutane sama da 1,000.
Kusan ko da yaushe ana zaman dar-dar da kallon hadarin-kaji tsakanin bangarorin biyu a kan iyakar Israi'lar da Lebanon, amma kuma ana ganin kowannensu a yanzu yana son kauce wa samun wani mummunan rikici.