Kotu ta soke zaben Alhassan Ado Doguwa

Doguwa

Asalin hoton, Facebook

An wallafa

Kotun wadda ke zamanta a Kaduna ta soke kujerar dan majalisa mai wakilatar Doguwa/Tudun Wada da ke jihar Kano, inda ta bayyana dukkanin zabukan da aka yi a kananan hukumomin guda biyu da yake wakilta da tafka kurararai.

Alkalin kotun Oludotun Adefope-Okojie, ya yanke hukuncin cewa a sake zabe a kananan hukumomin na Doguwa da Tudun Wada.

Kotun ta ce zaben bai inganta ba kasancewar hukumar zaben kasar ba ta bai wa wasu jam'iyyu dama ba a lokacin bayyana sakamakon zabe.

Yanzu haka kotun ta bai wa hukumar zabe kwanaki 90 domin ta sake gudanar da sabon zabe a kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada.

Tun da farko dai kotun sauraron kararrakin zabe ta yi watsi da karar da Yusha'u Salisu na jam'iyyar PDP wanda ya yi takara da Alhassan Doguwa bisa gaza gamsar da kotun kan zarge-zargen magudi.

To sai dai yanzu haka kotun daukaka karar ta ce ta yi mamakin yadda kotun sauraron kararrakin zaben ta yi watsi da shaidun da dan jam'iyyar ta PDP ya gabatar mata.

Wannan dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da wata kotun daukaka kara ta soke zaben dan majalisar Kiru/Bebeji, Abdulmuminu Jibril.