Muhammadu Buhari ya koma gida Najeriya

Asalin hoton, Twitter / @BashirAhmad
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Najeriya daga Birtaniya bayan wata ziyara da ya kai can.
Shugaban ya koma gida cikin daren Juma'a ne, kamar yadda Bashir Ahmad, mai yi masa hidima kan kafofin sada zumunta ya wallafa a Twitter:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Bashir Ahmad ya wallafa cewa: "Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja cikin daren yau bayan wata ziyara ta kashin kansa da ya kai Birtaniya".
Jirgin shugaban Najeriyar ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da karfe 9:45 na dare.
Ya kuma tattauna da manema labarai bayan saukar tasa.

Shugaban ya ce yana da kudurin ci gaba da aiki tukuru domin samar wa 'yan kasar abubuwa more rayuwa.
Shugaban na Najeriya ya tafi Birtaniya ne domin wata ziyara da aka ce ba ta aiki ce ba.
Ya isa can ne tun ranar 2 ga watan Nuwamba, inda aka shirya cewa zai koma gida ranar Lahadi 17 ga watan na Nuwamba.
Jirgin Shugaba Buhari ya bar filin jirgin sama na Stanstead da ke birnin Landan da misalin karfe 3:27 agogon Najeriya.












