An damke tsohon minista Adoke a Dubai

Hukumar 'yan sandan kasa da kasa watau Interpol ta damke tsohon ministan shari'ar Najeriya bisa zargi sa da hannu a wata badakalar cin hanci kan danyen mai na fiye da dala biliyan daya.
Lauyan Mr Mohammed Bello Adoke ya tabbatar da tsare tsohon ministan a Dubai, amma ya ce bisa wani sammaci ne da lokacinsa ya wuce.
A baya Mr Adoke ya ce bai ci komai ba game da wata yarjejeniyar sayar da wata rijiyar mai a shekara ta 2011.
A cikin watan Afrilu ne hukumar yaki da rashawa a Najeriya - EFCC ta ba da sammacin kama shi tare da tsohon ministan man kasar, Dan Etete da kuma wani manaja a kamfanin mai na Italiya mai suna Eni.
Lamarin ya janyo shari'a mai tsawo tsakanin gwamnatin Najeriya da wasu kusoshi a kamfanonin mai na Eni da kuma Shell.
Sai dai duk kamfanonin biyu sun musanta aikata ba dai-dai ba.
Mohammed Bello Adoke ya kasance tsohon ministan shari'ar Najeriya daga 2010 zuwa 2015.
A watan Disambar 2015 ne bayan barin su gwamnati, hukumar EFCC ta gayyace domin bayar da bahasi kan badakalar yarjejeniyar rijiyar man ta Malabu.
Hukumar ta yi masa tambayoyi kan kudi £22.5m da suka yi batan dabo wadanda aka karbo daga cikin irin wadanda aka zargin marigayi Sani Abacha ya sata ya jibge a tsibirin Jersey.












