Ambaliya ta shafe gidaje 700 a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, EPA
An wallafa
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyyar ambaliyar da ta mamaye unguwanni da wuraren hakar ma'adinai.
Akalla gidaje 700 ne ambaliyar ta yi awon gaba da su, baya ga daidaita jama'a a Pretoria, babban birnin kasar Afrika ta Kutu.
Ambaliayar ta kuma mamaye tashar wutar lantarkin yankin, abin da ya kawo tsaiko ga ayyukan lantarki a tashar.
Hakan ya tilsatsa dakatar da hakar zinare da lu'ulu'u.
Kamfanin harkar lu'ulu'u na Petra Diamonds ya ce ya dakatar da ayyukansa a karkashin kasa domin kauce wa barnar abaliyar.








