Ghana ta samu cimma wannan nasara ce ta hanyar bada gudummawarta a jadawalin tsarin sauyin yanayi na shekarar 2030

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Ghana ta sanar da rage tan miliyan biyu na gurbatacciyar iskar da take fitarwa daga ayyukan na gurbata yanayi.Wannan wata hanya ce da nuna cewa gwamnatin da gaske take wajen kama hanyar aiwatar da manufofin rage gurbatacciyar iska kamar yadda majalasar dinkin duniya ta yi shela.
Mukaddashin daraktan hukumar kare muhalli ta EPA, Mista John Epuaman shi ya sanar da hakan a wani bayani da ya gabatar a taron bita kan sauyin yanayi karo na takwas da ake gudanar wa a Spaniya.
Ya ce kasar ta Ghana ta samu cimma wannan nasara ce ta hanyar bada gudummawarta a jadawalin tsarin sauyin yanayi na shekarar 2030 a cikin wani tsari da tayi na tsara ci gaba na matsakaicin lokaci na shekara ta 2017 zuwa 2021.
Rahoton ya kara da cewa dafa abinci mai tsafta da rage fitar iskar gas zuwa sararin samaniya da kuma samar da wutar lantarki mara gurbata yanayi su ne suka bada gudummawa wajen samun cimma rage yawan gurbatacciyar iskar da aka fitar a kasar daga shekarar 2011 zuwa 2017.
Sai dai wannan mataki na gwamnatin Ghana ya haifar da cece-kuce inda masu fafutukar kare muhalli na kasar ke cewa babu wasu kwararan shaidu da gwamnatin ta nuna game da wannan kalami da ta yi ta hanyar bayar da wasu alkalumma game da lamarin.
A cewar Wasiu Ibrahim, idan aka duba rahoton da gwamnatin ta gabatar, babu wasu bayanai masu gamsarwa da zai kare matakinta.
Yace ya kamata gwamnati ta fito ta yi cikakken bayani kan matakan da ta bi wajen rage adadin gurbatacciyar iskar.








