Coronavirus: Babu dalilin hana wasanni a Ingila

Asalin hoton, Getty Images
Babu wani dalili mai kwari da zai janyo a dage wasanni a Burtaniya saboda Coronavirus, inji sashen lura da al'ada da kuma wasannin na kasar.
A wani taro da ya gudana tsakanin sashen lura da al'adun da kuma hukumar wasannin ta kasar ranar Litinin, an tattauna yadda za a tunkari annobar Coronavirus da kuma yadda za a hana taron mutane.
Babban sakon shi ne "daka mu kidime" inji shugaban hukumar kwallon zari ruga Bill Sweeney.
Yanzu dai Burtaniya ta gamsu da shirinta na tunkarar cutar bayan wannan trattaunawar gaggawa da aka yi kan cutar.
A safiyar Litinin ne sakataren hukumar al'adu na kasar Oliver Dowden ya ce, da yuwuwar harkar wasanni a Birtaniya ta fuskanci matsalar Coronavirus a kusa nan ba da dadewa ba.
Tuni mutane hudu suka mutu a Burtaniyan bayan kamuwa da cutar, an kuma gwada mutane sama da 300 an gano suna dauke da wannan cutar.
A makon da ya gabata ne, hukumar FA ta Ingila ta ce daga yanzu an daina gaisawar da ake idan za a fara wasan gasar, saboda gujewa cutar Coronaviru.








