Kasuwar cinikin ‘yan kwallo: Makomar Tierney, Faivre, Anderson, Barkley, Brahim da Fernandinho

Napoli na son daukar dan wasan Arsenal dan kasar Scotland Kieran Tierney bayan ta gaza daukar dan kwallon mai shekara 23 a farkon kakar wasan da ta wuce. (Telegraph - subscription required)
Manchester United na shirin kammala daukar dan wasan Paris St-Germain da ke murza leda a gasar 'yan kasa da shekara 22 Romain Faivre. (Sun).
Everton na duba yiwuwar zawarcin dan wasan Brazil mai shekara 27 Felipe Anderson, wanda yake zaman aro a Porto daga West Ham United. (Teamtalk).
Chelsea ba ta so ta bar dan wasan Ingila Ross Barkley ya koma Aston Villa baki daya - inda yake zaman aro na kakar wasa daya - domin kuwa har yanzu akwai sauran shekara biyu da rabi kafin kwangilar dan wasan mai shekara 27 ta kare. (Birmingham Mail).
Har yanzu akwai yiwuwar dan wasan Chelsea mai shekara 23 dan kasar Ingila Fikayo Tomori zai tafi Newcastle United, a yayin da yake shirin tafiya zaman aro a wannan watan. (Chronicle).
Dan wasan Sifaniya Brahim Diaz na shirin barin AC Milan a karshen wa'adin zaman aronsa inda zai koma Real Madrid, ko da yake kungiyar kwallon kafar Italiya tana so dan wasan mai shekara 21 ya ci gaba da murza mata leda. (Le10Sport - in French).
Dan wasan Ingila Jadon Sancho ya ce ya sha wahala a kakar wasan da ta wuce a Borussia Dortmund tun da aka alakanta shi da yunkurin tafiya Manchester United a bazarar da ta wuce, amma dan wasan mai shekara 20 ya yi amannar cewa yanzu ya koma ganiyarsa. (Manchester Evening News).
Wakilin dan wasan Manchester City Fernandinho ya yi watsi da rade radin cewa dan kwallon mai shekara 35 zai koma kungiyar kwallon kafar Brazil Athletico Paranaense idan kwangilarsa a City ta kare a bazara. (Globo Esporte - in Portuguese).
Fenerbahce tana son karbar £14m kan dan wasan Turkiyya Ozan Tufan a yayin da Crystal Palace da West Bromwich Albion da ma kungiyar CSKA Moscow suke sha'awar daukar dan wasan mai shekara 25. (Hurriyet - in Turkish).
Liverpool ta tattauna da kungiyoyin kwallon kafa a Belgium, Jamus da kuma Switzerland domin yiwuwar ba su aron dan wasan Netherlands mai shekara 19 Sepp van den Berg. (Goal).
Real Betis na son daukar dan wasan Southampton Dan N'Lundulu, wanda ya wakilci Ingila a matakin matasan 'yan wasa. Saura wata 18 kwantaragin dan kwallon mai shekara 21 ta kare. (TodoFichajes - in Spanish).












