Ƴan sanda sun kama wata mata mai yi wa ƙungiyar IPOB leƙen asiri

Asalin hoton, NIGERUA POLICE
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama wata mata mai suna Gloria Okolie da ake zargin tana da hannu a jerin hare-haren da aka kai da gangan a kan caji ofis na 'yan sanda da ofisoshin hukumar zaɓe ta INEC da kuma kisan jami'an tsaro a yankin Kudu maso Gabashin kasar.
Sanarwar da ke dauke da sa hannun mataimakin kakakin rundunar 'yan sandan Najeriyar, CSP Aremu Adeniran, ta ce wadda ake zargin, mai shekara 22, yar asalin garin Umutanza ne a jihar Imo.
Ya ce sun yi sanarar kama ta ne tare da hadin gwiwar sojoji da sauran jami'an tsaro.
Ya kuma ce an kama ta Gloria ne sakamakon binciken da aka yi da kuma kafuwar wata rundunar tsaro ta musaman da ake kira Operation Restore Peace, domin karya lagon mayakan IPOB da ke son ballewa daga Najeriya tare da dakile hanyoyin da suke samun miyagun kwayoyi da kuma makamai.
Binciken ya nuna cewa Gloria Okolie mamba ce ta kungiyar IPOB a jihar Imo, wacce ta yi aiki tare da wani Benjamin Uzoma Emojiri aka fi sani da "Onye Army", daya daga cikin kwamandojin kungiyar ta IPOB.
Jami'an tsaro na nemansa game da harin da aka kai wa hedikwatar rundunar 'yan sandan da hedikwatar hukumar kula da gidan yarin na jihar Imo, a cewar sanarwar.
Kamun nata da kuma bayanan da ta bayar sun taimaka wa 'yan sanda wajan kama Benjamin Uzoma Emojin, in ji CSP Aremu Adeniran.
Sanarwar ta kuma ce binciken ya nuna cewa Gloria Okolie ta yi amfani da jinsinta da kyawonta wajen gudanar da ayyukan leƙen asiri kan sojoji da 'yan sanda a madadin IPOB.
Ta kuma rika karbar tsabar kudi, da miyagun kwayoyi da makamai a madadin IPOB sannan ta kai wa kwamandojin kungiyar a sansanoninsu.
Sanarwar ta ce ta taka muhimmiyar rawa a kisan jami'an 'yan sanda da lalata dimbin dukiyoyin mutane.
CSP Adeniran ya ce za a gurfanar da Gloria Okolie gaban shari'a da zarar 'yan sanda sun kammala bincike.












