MDD: 'An sace miliyoyin daloli a Sudan ta Kudu mai fama da rikici'

Wani bincike da kwararru a Majalisar Dinkin Duniya a fanin shari'a suka gudanar, sun gano cewa 'yan siyasa, da sojoji da 'yan kasuwa a Sudan ta Kudu na karkatar da miliyoyin daloli asusun ajiyarsu na bankuna, ta hanyar amfani da rashin zaman lafiyar da kasar ke ciki.
Hukumar kare hakkin dan adam ta Sudan ta Kudu, ta ce akwai kwararan shaidun da ta ke da su da suka nun tun shekarar 2018, jami'an gwamnati da masu alaka da ita ke almubazzaranci da wawure gwamman miliyoyin daloli, sannan wanna adadi kadan ne daga cikin irin barnar da suka tafka.
Rahoton y ace wannan nau'in cin hanci da rashawar ta ke hakkin dana dam ne, da barazana ga tsaron kasar.
Haka kuma rahoton ya gano a dai shekarar 2018 din an karkatar da dala miliyan 7, zuwa wani asusun da ba a bayyana ba.
Don haka hukumar kare hakkin dana dam din ta ce kusan a wannan shekarar ban da sacearzikin kasa babu abin da jami'an gwamnati suka yi a Sudan ta Kudu, alhalin dubban 'yan kasar na fama da matsananciyar yunwa, yara bas a samun abinci mai gina jiki.
"Binciken mu ya gano yadda 'yan siyasa suka da sojoji da 'yan kasuwa sukai rub da ciki kan dukiyar kasa. Hatta manyan ma'aikatan bankuna da wasu tsiraru da ke kasashen waje sun samu na su kason ," Yasmin Sooka, shugabar hukumar a lokacin da ta ke gabatar da rahoton a Geneva.
A bangare guda kuma hatta fannin man fetur din kasar bai tsira ba, inda ake fitar da danyen mai daga Sudan ta Kudu ba tare da an shigar da bayanan kudi ko inda ya nufa ba. Sannan mazauna yankin da arzikin mai yak e na fama da gurbacewar muhalli, da haddasa tabarbarewar lafiyar mutane.
Wannan lamari dai na faruwa a jaririyar kasar da ba ta dade da karbar 'yancin kai daga kasar Sudan ba, kasar da ta yi fama da rikicin kabilanci tsakanin shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar, wadanda 'yan kabilar Dunka da Nuer ne.
Kuma kashi biyu cikin uku na al'ummar kasar na fama da bakin talauci, ya yin da sama da mutum miliyan 7 ke fadi tashin samun abin da za su kai bakin salati.
Har yanzu gwamnatin Sudan ta Kudu ba ta maida martani kan rahoton na kwararru na hukumar kare hakkin dan adam na kasar da hadin gwiwar hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya.












