CAN ta caccaki Amurka kan cire Najeriya daga cikin jerin masu tauye ƴancin addinai

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN ta caccaki kasar Amurka kan cire Najeriya daga cikin jerin masu tauye ƴancin addinai a ƙasar a shekarar 2021, tana mai cewa ce har yanzu kungiyoyin 'yan ta'adda da sauran kungiyoyin addinin musulunci na ci gaba da muzgunawa Kiristoci a kasar.
Uwar kungiyar kiristocin ta ce bayanai ko kididdiga da gwamnatin Amurka ta yi amfani da su wajen fitar da Najeriya daga cikin jerin ƙasashen da ake fuskantar wannan matsala musamman kan batun 'yancin addini ya bata mamaki.
A ranar Laraba sakataren harkokin wajan Amurka, Anthony Blinken ya fitar da wata sanarwa da ta bayanna Rasha da China da wasu kasashe takwas a matsayin masu keta hakkin adini, kuma ba bu sunan Najeriya a ciki wadda a shekarar 2020 tana cikin jerin kasashe da ake zargi suna musgunawa sauran addinai .
Abin da ya harzuka CAN
A ziyarar aiki da Blinken ya kai Najeriya wadda ta zo karshe a ranar Juma'a ya ce Amurka ta cire Najeriya sakamakon bayannai masu sahihanci
Sai dai a sanarwar da CAN ta fitar da ke dauke da sa hannun shugabanta Rabaran Samson Ayokunle ta nuna rashin jin dadinta akan matakin
Ta ce kawo yanzu ana ci gaba da kai wa kiristoci hare-hare musaman a arewacin kasar kuma matsalar ba ta sauya zani ba tun daga shekarar 2020 zuwa 2021 .
Sanarwar ta ce: "Gwamnatin Amurka ba ta tuntube mu ba a lokacin da ta sanya Najeriya cikin jerin kasashe da aka nuna damuwa a kansu game da ƴancin addinai, hakan nan ba su nemi ra'ayinmu ba kafin cire Najeriyar daga cikin jerin sunayen. Da sun yi haka da mun samu damar yin nazari kan kididdigar baya da ta yanzu a kan yancin addinai a Najeriya.
"Kiristoci har yanzu suna fuskantar musgunawa daga ISWAP da kungiyar Boko Haram . Wadannan kungiyiyoyi sun ce manufarsu ita ce su kawar da addinin Kirista daga Najeriya da kuma kafa Musulunci a matsayin addini daya tilo daga Arewa har zuwa tekun Atlantika a Kudu" in ji sanarwar ta CAN
Kungiyar ta CAN ta kuma ce 'yan fashin daji sun bi sahun wasu kungiyoyin Islama masu tsatsauran ra'ayi suna kai hare hare a coci-coci , suna kashe masu ibada tare da yin garkuwa da su domin karbar kudin fansa.
Kungiyar ta kuma ce duk da cewa matsalar ta shafi kowa da kowa amma da gwamnati ta dauki matakin dakile ta cikin sauri ba bata kai yadda take a yanzu ba..
Sai dai kungiyar ta yi zargin cewa gwamnatin kasar kawo yanzu tana tallafawa wasu kungiyoyin addinin Islama amma ta ki shiga cikin wasu kungiyoyin addininin kirista ta kasa da kasa.
"Ya zuwa yanzu, gwamnatinmu ta na bada tallafi kasancewarta mamba a kungiyoyin addinin musulunci irinsu OIC da sauransu ba tare da shiga cikin wata kungiyar addinin kirista ta kasar waje ba". In ji kungiyar.
Tun farko gwamnatin Najeriya ta ce batun sanya sunan kasar tun da fari a wannan jeri na kundin baƙin fentin Amurka sharrin masu rajin a-ware ne kan yaƙi da Boko Haram.
Ta kuma ce tana iya kokarinta wajan daukar mataki ,












