Kasuwar 'yan kwallop: Makomar Mbappe, Raphinha, Azpilicueta, Barkley, Digne, da Umtiti

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe ya ce ba zai bar PSG a watan Janairu zuwa Real Madrid ba har sai kakar wasannin bana ta kare. (CNN)
Su kuwa kungiyoyin Liverpool da Bayern Munich na takarar sayen dan wasan tsakiyar Leeds United Raphinha, duk da dan wasan bai shirya barin kulob dinsa ba a watan Janairu. (Mirror)
Barcelona kuwa ba ta cire ran yi wa 'yan wasa Chelsea Cesar Azpilicueta da Andreas Christensen kudin goro ba.(Sport - in Spanish)
Everton ta tattauna yiwuwar dauko dan wasan tsakiyar Chelsea Ross Barkley a matsayin aro. (Telegraph - subscription required)
A wata mai kama da haka Chelsea na son karbo mai tsaron bayan Everton din Lucas Digne, ganin cewa Ben Chilwell zai shafe lokaci mai tsawo yana jinya. (90 Min)

Asalin hoton, Getty Images
Har wayau a Ingila Newcastle ta shirya taya mai tsaron bayan Faransa da Barcelona Samuel Umtiti. (Marca)
Haka ma jaridar(Mirror) ta ruwaito cewa Newcastle din na da sha'awar sayen Gabriel Barbados da ke wasa a Flamengo da ke Brazil.
Idan muka leka Italiya (Sky Sport Italia, via Football Italia) ta ruwaito cewa dan wasan gaban Napoli Lorenzo Insigne zai iya barin kungiyar a karshen kaka, don tuni ya samu tayi daga Toronto FC da ke Amurka.
Juvnetus kuwa na son sauya wasu sharuda da ke kunshe a kwantiragin Paulo Dybala, wanda ka iya barin kungiyar a kyauta. (La Gazzetta dello Sport, via Football Italia)
A nan kuma Queens Park Rangers na gaban Nottingham Forest wurin neman sayen Steve Cook na Bournemouth. (Mail)












