Za a kashe N36m wajen binciken cutar ƙoda a Kano da Jigawa da Yobe

An wallafa

Ƙwararru a Jami'ar Tarayya ta Dutse a Najeriya na shirin soma wani bincike na tsawon shekarun biyu don gano mussabbabin samun yawaitar cutar ƙoda kwarin Hadejia da ke arewacin kasar.

Fiye da shekaru 20 ke nan da aka lura da yawaitar masu cutukan ƙoda a yankin abin da kuma ya yi sanadin mutuwar da yawa daga cikinsu.

Yankin dai ya kunshi wasu bangarori na jihohi uku wato Kano, da Jigawa, da kuma Yobe.

A cewar wanda zai jagoranci binciken, Dr. Muhammad Auyo, Shugaban Sashen Nazarin hallittu, da tsirarai da dabobi na Jami'ar, za afara binciken a watan Fabrerun 2022, Kuma tawagogi uku na kwararru ne za su gudanar da bincike.

"Tun shekaru 20 zuwa 30 da suka wuce ne muka fara fuskatar wadannan matsalolin," inji masanin inda ya ƙara da cewa shi kansa ya rasa danginsa 6 zuwa 7 wadanda duka cutar ƙodar ce ta yi sanadin mutuwarsu.

Gidauniyar tallafawa manyan makarantu da jami'o'in Najeriya wato TETFund ce dai ta ba kwararrun wani tallafin kudi na naira miliyan 36 don gudanar da binciken.