An yi wa Turawan da suka kashe Ahmaud Arbery ɗaurin rai-da-rai

Asalin hoton, Courtesy Arbery family
Wata kotu a Amurka ta sami wani uba da dansa da laifin kashe wani bakar fata yayin da yake gudun motsa jiki.
Kotun ta sami Travis da dansa Gregory McMichael da wani makwabcinsu William Bryan da laifin kashe Ahmaud Arbery saboda kawai shi bakar fata ne a watan Fabrairun 2020.
Dukkan mutanen, wadanda turawa ne za su shafe sauran kwanakin da suka rage mu su a gidan kurkuku, sai dai mutum na uku na iya neman a sako shi bayan shekara talatin
Kamar dai shari'ar nan da aka yi wa dan sanda Derek Chauvin wanda ya kashe bakar fatan nan George Floyd, wannan shari'ar ma ta ja hankalin duniya.
Ga yawancin wadanda suke bibiyar shari'ar, halayyar wadannan turawa ukun tunatarwa ce ga wani zamani da turawa kan rika farautar bakaken fata kuma su kashe su ba tare da sun aikata wani laifi ba.
Yayin da yake yanke musu hukunci, alkalin kotun ya ce turawan uku sun katse rayuwar wani dan Adam din da ba su da damar katsewa, kuma ya koka kan irin rashin imanin da mutum biyu na farko - wato Gregory McMichael da dansa Travis McMichael suka nuna wa Ahmaud Arbery:
"Ranar 20 ga watan Fabrairun 2020, kusan shekara biyu da ta gabata, aka harbe Ahmaud Arbery wanda mazaunin Glenn County ne, dalibin da aka yaye a makarantar Brunswick High ne, da ne kuma dan uwa ne, kuma matashi ne mai yakinin yin wani abu da rayuwarsa nan gaba."
A karkashin dokar jihar Georgia, daurin rai-da-rai ne hukunci mafi kankanta da alkalin zai iya yanke wa wadannan turawan uku.
Ya yi wa mahaifi Gregory mai shekara 66 da dansa Travis mai shekara 35 daurin da za su shafe sauran kwanakinsu a daure cikin kurkuku, inda mutum na uku kuwa sai bayan shekara 30 za a duba batunsa.
Mahaifiyar Ahmaud Arbery, Wanda Cooper Jones ta bayyana yadda ta ji bayan da aka yanke wa turawan uku hukuncin:
"Yayin da aka fara wannan shari'ar ranar 18 ga watan Oktoba, sai da na shafe makonni biyar a jere ina zuwa kotu a jere. Amma na san daga baya za mu sami nasara. Ban yi shakka ba. Kuma na san wannan ranar za ta zo. Na gode wa dukkan wadanda suka taimaka min da wadanda suka tsaya tare da ni yayin wannan lokaci mai matukar wahala."
Dukkan mutanen uku sun ce za su daukaka kara, sai dai akwai wasu batutuwan da za su fuskanci shari'a a kansu a gaban wasu kotunan gwamnatin tarayyar Amurka, kuma zai yi wuya wata kotu ta rage tsanannin wannan daurin.












