FIFA: Najeriya ta dawo na uku a iya kwallo a Afrika

An wallafa

Najeriya ta dawo na uku a jerin kasashen da suka fi kwarewa a fagen kwallon kafa a nahiyar Afrika.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta kuma mayar da Najeriya na 32 daga na 36, duk da ba ta yi nisa ba a gasar cin kofin najiyar Afrika ta AFCON da aka kammala a Kamaru.

Najeriya na bin bayan kasashen Senegal wadda ta dade a na daya, sai kuma Morocco ke binta.

A kasan Najeriya kuma akwai Masar da Tunisiya da Kamaru da Aljeriya da Mali da kuma Ivory Coast.

Sai dai a matakin duniya itama Senegal wadda ta lashe kofin gasar nahiyar Afrika makon da ya wuce ta dawo na 18 daga na 20.

To amma Aljeriya da ta lashe kofin AFCON na 2019 ta kara yin kasa zuwa na 43, yayin da Mali ta koma na 48, sai kuma Ivory Coast na 51.

A teburin na FIFA Belgium ce ke ci gaba da zama ta daya, sai Brazil, Faransa, Argentina, Ingila, Sfaniya, Focugal, Denmark da kuma Holand.

Kasashen duniya na ci gaba da damarar zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar cikin watan Nuwamba, yayin da wasun su ke shirin buga zagayen karshe na wasan share fagen zuwa gasar.

A watan Maris mai kamawa ne tawagar Super Eagles za ta buga da takwararta ta Black Stars ta Ghana gida da waje, a kokarin neman gurbin zuwa Qatar 2022.