Liverpool ta doke Leicester 2-0, Arsenal ta koma na biyar

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta rage yawan makin da Manchester City ta bata, bayan da ta doke Leicester City da ci 2-0 a gasar Premier League.
Diogo Jota ne ya ci kwallayen biyu a filin Anfield a minti na 34, kafin ya ci ta biyu a a minti na 87.
Hakama a karon farko tun kafin fara wasan cin kofin nahiyar Afrika, magoya bayan Liverpool sun shedi dawowar shahararren dan wasan gabansu Mohamed Salah.
Salah ya wakilci kasarsa Masar a gasar wadda suka yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Senegal.
A yanzu Liverpool ta rage yawan makin da Manchester City ta bata daga 12 zuwa tara, kuma tana da kwanton wasa daya.
A jiya ne Manchester City ta doke Brentford da ci 2-0 wanda hakan ya bata damar kara matsawa kan teburi kafin wasan na yau.
A daya wasan da aka buga ranar Alhamis Arsenal ta je har gidan Wolves da doke ta 1-0.
Nasarar ta sa Gunners sun koma na biyar a teburin Premier League da maki 39 a wasanni 22.
A ranar Asabar Manchester City za ta tafi gidan Norwich, yayin da Liverpool kuma za ta kai ziyara gidan burnley.












