Rikicin Ukraine: Yan wasan Rasha da Belarus za su buga wasannin Paralympics

Asalin hoton, Getty Images
Yan wasan tsalle-tsalle daga kasashen Rasha da Belarus za su samu damar halartar wasannin Olympics na masu nakasa amma a karan kansu, in ji hukumar shirya wasannin ta IPC.
Hukumar ta ce za su shiga gasar ba tare da tuta ba, kuma sunansu ba zai fito a jerin wadanda suka lashe sarka ba.
A ranar Juma'a ne za a kaddamar da gasar a birnin Beijing na China, a kuma fara wasannin ranar Asabar.
Duk wannan na zuwa ne saboda kutsen da Rasha ta yi cikin Ukraine, tare da hadin kan Belarus inda ake ci gaba da yaki.
Shugaban IPC Andrew Parsons ya ce kololuwar hukuncin da za su iya yi wa yan wasa daga kasashen kenan kamar yadda kundin hukumar ya tsara.
''IPC ta damu matuka da saba ka'idoji da gwamnatocin Rasha da Belarus suka yi, yayin da ake shirin fara gasar Beijing 2022.'' In ji Parsons.
Ya kara da cewa ''bayan yin tir da hakan, IPC ta yi amfani da damar da kundin gudanar da ita ya bata na kaucewa shiga batun da ya shafi siyasa.''

Matakin da IPCn ta dauka zai shafi yan wasa 71 daga kasashen na Rasha da Belarus hadi da tawagoginsu- dukansu ba za su yi amfani da sunan kasashen ba.
Hakama Hukuma ta bukaci a nuna wa yan wasan kasashen kulawa kamar sauran yan wasa da suka zo daga sauran kasashen duniya.
To amma ministar wasannin Burtaniya Nadine Dorries ta nuna matukar bacin rai da matakin IPC.
Ko a 2018 yan wasan Rasha sun tafi wasannin Paralympics a kashin kansu ne saboda kama kasarsu da hannu a amfani da kwayoyin kara kuzari da aka haramta.












