Yadda aka sace matafiya 38 cikin motocin bas biyu

Haitian Police

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

A kasar Haiti, an sace wasu mutum 38 matafiya a cikin wasu motocin bas biyu a wajen birnin babban birnin kasar Port-au-Prince.

Babu cikakken bayani kan ko a bukaci 'yan uwan mutanen su biya kudin fansa kafin a sako su.

Wannan lamarin ya auku ne kan babbar hanyar da ke hada babban birnin da kudancin kasar -- hanyar da kungiyoyi masu aikata laifuka ke iko da ita tun farkon wannan watan.

Ana ba direbobin moitocin safa shawarar kauracewa hanyar, sai dai ga yawancin mutanen da ke zama ko yin aiki a yankin, wannan shawara ce da ba za ta karbu ba.

Cikin shekara biyun da ta gabata, matsalar satar mutane domin karbar kudin fansa a Haiti sai karuwa ta ke yi, yayin da kasar ke fuskantar tabarbarewar tattalin arziki da na siyasa.

Barayin daji kan bukaci a biya su daruruwan dubban daloli kafin su saki wadanda suka sace.

Sannan lamarin ya kara kazancewa tun bayan kisan gillar da aka yi wa Shugaba Jovenel Moise watanni 11 da suka gabata.