West Ham ta kusan kammala ɗaukar Guilherme daga Palmeira

West Ham

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

West Ham ta kusan kammala ɗaukar matashin ɗan wasan Brazil mai shekara 18 Luis Guilherme daga Palmeiras kan £25.5m.

Daraktan tamaular West Ham, Tim Steidten yana Brazil, domin sayo ɗan ƙwallon don bunkasa ƴan wasan da Julen Lopetegui zai ja ragama.

Duk da cewar da ƙyar West Ham ta ɗauki Guilherme kamar yadda ake hasashe, to amma an sanar da BBC cewar ta kusan kammala cinikin.

Ɗan ƙwallon zai zama na farko da West Ham za ta ɗauka tun bayan da David Moyes ya bar ƙungiyar ta maye gurbinsa da Lopetegui a karshen kakar nan.

Steidten shi ne yake kula da dukkan cefanen da West Ham ke yi ta wajen saye ko sayar da ɗan wasa.

Guilherme ya fara buga wa Palmeiras wasa yana da shekara 17 da haihuwa a 2023, wanda ya buga wa ƙungiyar Copa Libertadores karawar cikin rukuni.