Ba za mu kori Graham Potter ba - Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu masu Chelsea na goyon bayan aikin Graham Potter, duk da kwasar kashi da kungiyar ke yi a wasannin bana karkashin jagorancinsa.
Chelsea ta ci wasa biyu daga 14 da ta yi a baya-bayan nan, wadda ta yi rashin nasara ranar Asabar a Premier a hannun Southampton ta karshen teburi.
Cikin watan Satumba aka nada tsohon kociyan Brighton a matakin wanda ya maye gurbin Thomas Tuchel, wanda ta sallama.
Masu Chelse sun ce sun bai wa Potter ragama ne kan kwantiragi mai tsawo, domin ya samu dawo da kungiyar kan ganiya cikin natsuwa.
Chelsea ta kashe fam miliyan 583, wajen sayo sabbin 'yan wasa a kasuwa biyu da aka yi cinikin 'yan kwallon tamaula a wasu kasashen Turai.
Ko a cikin watan Janairun 2023, kungiyar Stamford Bridge ta dauko karin sabbin 'yan wasa takwas - har da Enzo Fernandez mafi tsada daga Benfica.
Wasu na cewar rauni da 'yan wasan Chelsea da dama dake jinya shine ya jefa kungiyar a wannan halin na rashin kokari a kakar nan.
Wadanda ke jinya sun hada da kyaftin Cesar Azpilicuueta, wanda ya ji rauni ranar Asabar a karawar da Southampton ta ci Chelsea 1-0. a Premier League
Sauran da ke jinya sun hada da Raheem Sterling da Kalidou Koulibaly da N'Golo Kante da Mateo Kovacic da Christian Pulisic da Wesley Fofana da Edouard Mendy da Denis Zakaria da kuma Armando Broja.
Makomar Potter a Stamford Bridge ba za a aunata ba da rashin kokarin kungiyar a Champions League a bana ko kasa samun gurbin buga gasar badi ba.
Potter ya bar Brighton ya karbi aikin kociyan Chelsea kan yarjejeniyar kaka biyar, bayan da ta sallami Tuchel.
Chelsea ta yi nasara a karawa tara daga 25 karkashin Potter, tana ta 10 a Premier League da tazarar maki 10 tsakaninta da masu neman gurbin Champions League a kakar badi.
Ranar Asabar Chelsea za ta buga wasan hamayya da Tottenham a gasar Premier karawar mako na 25.












