Inter na fatan daukar Serie A na bana a kan Milan na 20 jimilla

Inter Milan

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

AC Milan za ta karbi bakuncin Inter Milan a gasar Serie A, ranar Litinin a karawar hamayya ta 'yan birnin Milan a San Siro.

Wannan shi ne wasa na biyu da za su fuskanci juna a Serie A a bana, bayan da Inter ta ci 5-1 ranar 16 ga watan Satumbar 2023.

Inter ta ci kwallayen ta hannun Henrikh Mkhitaryan da ya zura biyu da Marcus Thuram da Hakan Calhanoglu a bugun fenariti da kuma Davide Frattesi, wanda ya ci na biyar a raga.

Ita kuwa Milan ta zare daya ta hannun Rafael Leao a wasan na hamayya na 'yan birnin Milan masu wasa a San Siro.

Inter na fatan daukar Scudetto na bana, kuma a karon farko a kan Milan a tarihin babbar gasar tamaula ta Italiya.

Inter ce ta daya a kan teburi da tazarar maki 14 tsakaninta da Milan, kuma saura wasa shida a karkare kakar bana.

Wasa daya Inter za ta ci ta dauki Scudetto na bana, kuma za ta lashe da wuri tun kan kammala kakar nan, kamar yadda Napoli ta yi a bara.

Cikin wasa 32 da ta buga a lik ta ci 26 da canjaras biyar aka doke ta wasa daya a bana, kaka ta hudu a tarihi da ta yi irin wannan namijin kokari a babbar gasar tamaula ta Italiya.

Karawa dayan da aka doke ta a lik ita ce 2-1 da Sassuolo ta yi nasara a San Siro ranar Laraba 27 ga watan Satumbar 2023.

Simone Inzaghi, wanda ya fara aikin horar da Inter ranar 7 ga watan Yulin 2021 na daf da lashe Serie A na farko a tarihi, kuma na 20 da kungiyar za ta dauka jimilla.

Kenan Inter za ta lashe Scudetto na 20, za ta zama ta biyu a Italiya, bayan Juventus da za ta saka tauraruwa ta biyu a gaban rigarta.

Haka kuma Inter ta zura kwallo a raga a wasa 40 a Serie A, saura karawa hudu a gabanta ta kamo bajintar Juventus da ta yi.

Inter mai maki 83 ta ci kwallo 77 an zura mata 17 a raga, yayin da Milan ta biyu mai maki 69 ta ci 63 an kuma zura mata 37 a raga kawo yanzu.

Haka kuma wasa biyar baya Inter ce ke nasara a kan Milan, amma a wannan karon da zarar an doke Milan kenan Inter za ta lashe Scudetto na bana kenan.

Jerin wadanda suka lashe Serie A

  • Juventus FC 36
  • AC Milan 19
  • Inter Milan 19
  • Genoa 9
  • Torino 7
  • Bologna 7
  • Pro Vercelli 7
  • Napoli 3
  • AS Roma 3
  • Lazio 2
  • Fiorentina 2
  • Sampdoria 1
  • Hellas Verona 1
  • Cagliari Calcio 1
  • FBC Casale 1
San Siro

Asalin hoton, Getty Images

Wadanda suke kan gaba a cin kwallaye a Serie A:

  • Lautaro Martinez Inter Milan 23
  • Dusan Vlahovic Juventus 16
  • Albert Gudmundsson Genoa 13
  • Victor Osimhen Napoli 13
  • Olivier Giroud AC Milan 13
  • Paulo Dybala AS Roma 12
  • Duvan Zapata Torino 12
  • Marcus Thuram Inter Milan 11
  • Hakan Calhanoglu Inter Milan 11
  • Teun Koopmeiners Atalanta 11
  • Romelu Lukaku AS Roma 11