Champions League: Mbappe ya samu rauni

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gaban PSG da Faransa Kylian Mbappe ya samu rauni, kasa da makonni biyu a buga wasan zagayen kungiyoyi 16 a gasar Zakarun Turai.
Duk da PSG ta ci wasanta da Montpellier 3-1 ranar Laraba, ta fuskanci cikas bayan da aka fitar da Mpabbe kafin hutun rabin lokaci yana dingishi.
Kafin a cire Kylian sai da ya barar da bugun Fenareti har sau biyu.
Sai dai da yake magana bayan kammala wasan, koci Christopher Galtier ya ce raunin bai yi kama da mai muni ba.
To amma za a jira a ji abinda likitoci za su ce game da munin raunin ko akasin haka.
Wannan na zuwa yayin da ya rage kasa da mako biyu PSG ta fuskanci Bayern Munich a zagayen kungiyoyin 16 na gasar Zakarun Turai.
PSG ce za ta fara karbar bakuncin Bayern Munich a Paris ranar 14 ga watan Fabrairu, kafin su kwashi yan kallo a Alliance Arena da ke Munich ranar 8 ga watan Maris.








