An bai wa ma'aikata hutu saboda tsananin zafi a Iraki

Asalin hoton, EPA
Firai ministan Iraki Haider al-Abadi, ya bai wa dukkan ma'aikatan gwamnati umarni ka da su je aiki ranar Alhamis, saboda tsananin zafin da ke yi, irin wanda ba a cika yi ba.
Masu hasashen yanayi suna tsammanin yanayin zafi a ranar Alhamis a babban birnin kasar Baghdad, zai kai maki 50 a matakin salshiyas.
Baya ga birnin Baghdad, ana kuma tsammanin za a yi tsananin zafi a biranen Basra da Mosul.
Tsananin zafin zai iya jawo rashin wutar lantarki, wanda hakan zai sanya mutane cikin tsanani, da zai tsayar da al'amuran kasuwanci da sana'o'i.
A makonni baya-bayan nan dai an yi ta tsananin zafi a yankin Gabasa Ta Tsakiya, har hakan ya dan shafi wasu sassa na Turai.
Masana kimiyya sun yi gargadi cewa yanayin tsananin zafin zai iya jawo mutuwar mutum 52,000 duk shekara a Turai nan da shekarar 2100, idan har ba a yi wata hobbasa don dakatar da










