Daure mashaya wiwi ba shi da alfanu — Obasanjo

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya yi kira a daina daure kananan mashaya wiwi, yana mai cewa hakan na mayar da su manyan masu aikata laifuka.
Cif Obasanjo ya shaida wa BBC cewa a lokacin da aka daure shi a gidan yarin Najeriya ya hadu da mutane da dama wadanda laifinsu bai wuce "kama su da kullin wiwi ba, amma aka daure su".
A cewarsa, "Idan matashi ya soma shan wiwi kuma aka kama shi aka daure a gidan yari bai fito a matsayin babban mai aikata laifi. Maimakon haka, ya kamata a ba su kulawa ta musamman; a ji ta bakinsu, a rarrashe su domin su daina yin abin da suke yi".
Tsohon shugaban na Najeriya na magana ne a daidai lokacin da wata kungiya mai suna The Global Commission on Drug Policy - wacce fitattun shugabannin duniya ke cikinta, ta yi kira a sake yin nazari kan yadda ake magance matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Kungiyar, wacce ta fitar da sabon rahoto kan yadda ake tunkarar yaki da miyagun kwayoyi, ta ce tsangwamar da ake yi wa masu shaye-shayen kwayoyin tana yin kafar-ungulu a yakin da ake yi da kwayoyin.
Cif Olusegun Obasanjo shi ne shugaban kungiyar reshen Afirka ta Yamma.








