City na son daukar Aymeric Laporte

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Manchester City na fatan kammala daukar mai tsaron bayan Athletic Bilbao Aymeric Laporte a kan kudi fam miliyan 57.
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya nuna muradinsa a akan daukar dan kwallon mai shekara 23 kuma yana fatan kammala cinikin.
An fara cimma matsaya a kan yarjejeniyar, sai dai ana sa ran za a kammala cinikin kafin a rufe kasuwar musayar 'yan tamaulan ranar Laraba.
Yanzu dai Kevin de Bruyne ne dan wasa mafi tsada a kungiyar wanda aka saya a kan kudi fam miliyan 55 a 2015.








