''Yan Birtaniya za su yi zanga-zanga' yayin ziyarar Yariman Saudiyya

Asalin hoton, AFP
Yarima mai jiran gado na Saudiyya ya fara ziyarar kwana uku a Birtaniya a lokacin da ake tsaka da shirya zanga-zangar nuna adawa da rawar da kasarsa ke takawa a yakin Yemen.
Ana ganin Mohammed bin Salman mai shekara 32, a matsayin wanda ke son kawo sauyi a al'adun kasashen Larabawa masu arziki.
Birtaniya na son yin amfani da damar da Saudiyya ta bude a bangaren tattalin arziki, amma kuma za ta nuna damuwarta kan halin ha'ula'i da ake ciki a Yemen.
Ana sa ran mutane za su yi zanga-zangar a wajen fadar Birtaniya da ke Downing Street, don nunawa fushinsu kan kashe fararen hula da ake a Yemen sakamakon hare-haren da rundunar sojin hadaka da Saudiyya ke jagoranta ke kai wa - wanda Birtaniya da Amurka ke goyawa - a yaƙin da suke da 'yan tawayen Houthi.
Yariman, wanda ake zaton shi ne magajin gadon Sarki Salman mai shekara 82, yana ziyara ne a karon farko a Birtaniya tun bayan zamowarsa yarima mai jiran gado.
Zai kuma ci abincin dare tare da Mijin Sarauniya Izabel da jikanta Yarima William.
Ana danganta Yariman da mai kawo sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewa a kasar da ta ke mai ra'ayin 'yan mazan jiya, kamar janye dokar hana mata tuka mota.
Har ila yau, ya kaddamar da yaki da cin hanci da rashawa a kasar, al'amarin da ya sa aka tsare yarimomi da ministoci da kuma manyan 'yan kasuwa wadanda aka samu kimanin dala biliyan 106 a hannunsu.
Duk da haka, mutane da yawa sun soki matakinsa na shiga fadan Yemen da kuma takunkumin da ya sanyawa Qatar, tare da dakatar da masu adawa da manufofinsa.
Za a kafa sabuwar majalisar hadin gwiwa da za ta iya kawo Saudiyya ta zuba jarin fam biliyan 100 a kasar Birtaniya a cikin shekaru 10 masu zuwa.













