Allah Ya jikan Malam
A nan muka kawo karshen sharhin da muke kawo mu ku kai-tsaye, kan jana'izar Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u.
Karanta bayanai da labarai game da yadda aka gudanar da jana'izar jagoran Darikar Tijjaniya a Afirka, Khalifa Sheikh Isyaka Rabi'u, a birnin Kano.
Abdulwasiu Hassan and Halima Umar Saleh
A nan muka kawo karshen sharhin da muke kawo mu ku kai-tsaye, kan jana'izar Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u.

Asalin hoton, Bashir Ahmed

Kamfanin da marigayin ya kafa na Isyaku Rabiu & Sons a matsayin kamfani mai kasuwancin gine-gine da harkar inshora da na banki da kuma saye da sayarwar filaye.
A shekarun 1970, kamfanin ya zuba jari cikin harkar hada akwatuna da jakukkuna, kuma wannan wani hadin gwuiwa ne da wasu masu zuba jari daga Lebanon.
A 1972 ya kafa masakar Bagauda Textile Mill, masu saka zannuwa da kayan inifom, inda daga nan ne ya kafa wasu kamfanonin da ke kasuwanci a bangarori daban-daban na tattalin arzikin kasar.
Wasu daga cikin sassan sun hada da kasuwanci kan kifi, da harkar gidaje da filaye, da siga, da kamfanin da ke samar da kayan motoci musamman na Daihatsu.
Amma saboda faduwar darajar Naira, kamfanin ya mayar da hankalinsa wajen kere-kere da kasuwanci kaya.
Marigayi Isyaku Rabi'u ya rasu ya bar mata da 'ya'ya har da jikoki masu yawa, kuma a cikin 'ya'yansa akwai Nafiu Rabiu, wanda shi ne babban dansa. Akwai kuma babban dan kasuwan nan, Abdulsamad Rabiu, wanda shi ne shugaban kamfanonin BUA.
Akwai kuma Rabi'u Rabi'u, mai kamfanin jirgin sama na IRS Airlines, da Naziru Rabi'u, da Quraish I Rabi'u, da Makiu Rabi'u, sai Abdullahi Rabi'u, da Muhammad Rabi'u, da Daha Rabi'u.
Kuma a fili yake cewa gidan marigayin na cikin gidaje mafi girma a duk fadin Kano.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, mustapha Ibrahim Facebook

Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u ya samu daukaka a rayuwarsa ta fannoni da dama.
Ya yi fice a fagen karatun Alku'ani da yi masa hidima abin da ya sa ake masa lakabi da "Khadimul Kur'an".
Ya kuma shahara wurin kafa makarantu da masallatai musamman a birnin Kano da kewaye.
Daga bisani kuma an nada shi Khalifan Darikar Tijjani a Najeriya saboda irin gudummawar da yake bayarwa a wannan fage.
Sai dai har ya rasu ana ja-in-ja tsakanin jama'arsa da na Sheikh Dahiru Usman Bauchi kan wane ne ya fi cancantar wannan mukami.
Ya kuma yi suna wurin tallafawa marayu da marasa galihu.
Marigayin, wanda amini ne ga marigayi Sarkin Kano Ado Bayero, da Alhaji Aminu Dantata, yana daga cikin fitattun dattawan da suka rage a jihar.

Asalin hoton, Other
An tsoshe titin Goron Dutse saboda cinkoson mutane a wajen jana'izar Marigayi Khalifa Isyaka Rabiu

Yawan cunkoson da aka smau a wajen binne marigayin ya sa wasu manyan masu fada a ji na Najeriya ba su samu shiga wajen da aka binne shi ba, ciki har da shahararren mai kudin nan, Aminu Dantata, da wasu manyan mutane.
Gwamnonin jihohin Neja da Jigawa da Kano ne kawai suka samu shiga, sai kuma 'ya'yansa da wasu daga cikin jikokinsa.
Manyan 'ya'yansa hudu ne suka saka shi a kabarinsa, wato Nafi'u da Abdussamad da Rabi'u (Alhaji Karami) da kuma Naziru.

Hotunan uwargidan shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari a yayin da ta je Kano don yi wa iyalan Khalifa Isyaka Rabi'u ta'aziyyar mutuwarsa a ranar Juma'a.

Asalin hoton, Aisha Buhari

Asalin hoton, Aisha Buhari

Asalin hoton, Aisha Buhari

Asalin hoton, Aisha Buhari

Asalin hoton, Aisha Buhari

Asalin hoton, Aisha Buhari

Asalin hoton, Aisha Buhari
Saboda cincirindon mutane da kyar aka samu shigar da Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje wajen binne gawar Marigayi Khalifa Isyaka Rabiu.

An binne marigayin a makabartar gidansa da ke Kano.
"Yanzun nan na ziyarci iyalan Marigayi Khalifa Sheikh Isyaku Rabi'u a jihar Kano, babban malamin addinin musuluncin nan, don mika ta'aziyyata kan wannan rashi da ba za a mayar da kamarsa ba.
Ina yi wa daukacin al'ummar Kano da iyalan marigayin ta'aziyyar wannan rashi, da fatan Allah ya ji kansa," a cewar Hajiya Aisha Buhari.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram
Uwargidan shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta isa Kano don yin ta'aziyyar rasuwar marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u.

Asalin hoton, Aisha Buhari Instagram
Ana ci gaba da aike da sakonnin ta'aziyya ga iyalan marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u daga ciki da wajen Najeriya.
Shugaba Buhari wanda ba ya kasar a yanzu, ya nuna matukar alhininsa tare da yin addu'ar Allah ya ji kan mamacin.
Shi ma tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida ya ce ya kadu da jin rasuwar Khalifa saboda irin shakuwar da ke tsakaninsu tsawon shekaru.
Ya yi addu'ar Allah ya jikansa ya gafarta masa, Ya kuma bai wa iyalansa hakurin wannan babban rashi.

Asalin hoton, IBB twitter
Cincinrindo mutane ya hana a isar da gawar Khalifa Isyaka Rabiu inda za a binne ta a gidansa.

A yanzu an kammala Sallar Jana'izarsa, za a binne shi a cikin makabartar da ke cikin gidansa a Kano

A yanzu dai an tayar da sahu don gabatar da sallar gawar marigayin.