Bankwana
Masu bibiyarmu sai da mun hadu gobe in da rai da lafiya.
Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Ahmad Tijjani Bawage
Masu bibiyarmu sai da mun hadu gobe in da rai da lafiya.

Kafafen yada labaran kasar Habasha sun yi gargadin cewa, sama da mutane miliyan takwas suna fuskantar barazanar matsanancin kamfar ruwa, a wasu bangarori na arewa maso gabashin Jahar Amhara, waɗanda ke fuskantar mummunan tasirin yakin Tigray mai makwabtaka.
Jami'an shiyyar sun ce, kimanin tashoshin samar da ruwan sha 1500 ne aka lalata a yakin da aka gwabza tsakanin dakarun gwamnati da mayakan 'yan tawayen Tigrayan.
An kawo karshen tashin hankalin ne a watan Nuwamba, sai dai yakin ya bar baya da kura, sakamakon karancin abinci da ruwan sha, da cibiyoyin kiwon lafiya, da ake fama dashi a dukkan bangarorin na Tigray da Amhara.
Karkashin yarjejeniyar zaman lafiyar, mayakan Tigrayan sun amince su aje makamansu, amma har yanzu akwai mayakan dake tittidowa daga kasar Eritrea mai makwabtaka, dake kara mamaye shiyyar.

Tsohon firaministan Pakistani, Imran Khan, ya yi gargadin cewa, kasarsa zata iya fadawa cikin halin durkushewar tattalin arziki kamar kasar Sri Lanka.
Khan ya fada wa BBC cewa, aiwatar da babban zabe a kasar ne kadai zai iya zama mafita.
"Alal hakika, aikin gama ya gama. Al'amurra zasu kara sakwarkwacewa idan wannan gwamnati ta kai wa'adi mai tsawo. Babban abin damuwar shine, Pakistan zata iya tsintar kanta cikin makamancin yanayin da Sri Lanka ke ciki. Hanyar da Pakistan zata daidaita yanayin tattalin arzikinta shine ta gudanar da sahihin zabe."
Khan wanda ya sauka daga mukamin firaninstan kasar a watan Afrilun bara, bayan kada kuri'ar yanke kauna, tun daga wancan lokaci yake ta hankoron neman sake komawa kan madafun iko.
Pakistan na fama da matsalar tabarbarewar tattalin arziki mafi muni.
Gwamnatin kasar ta zargi manofofin da Khan ya bullo dasu a lokacin da yake kan mulki da cewar sun kara lalata yanayin tattalin arzikin kasar.

Asalin hoton, Getty Images
Kasar Faransa tana kara fuskantar tabarbarewa al'amurra, a yayin da kungiyoyin kwadago ke kara dunkulewa, kwana guda da barkewar a fadin kasar domin nuna adawa da shirin garambawul na shugaba Macron a tsarin fansho na kasar.
Yan sanda a kasar suna sa ran sama da mutane dubu 300 zasu fito zanga zangar, sai dai kungiyoyin kwadagn sun ce adadin zai iya kaiwa miliyan guda.
Yajin aiki ya haifar da tsaiko a tashoshin jiragen kasa, da soke tashin jiragen sama, ya kuma shafi hatta ayyukan matatun man fetur din kasar.
Kaso biyu bisa uku na mutanen Faransa suna adawa da sabon tsarin garam-bawul na kara shekarun ritaya a kasar daga shekaru 62 zuwa 64: Jean-Luc Mélenchon, shugaban gamayyar kungiyoyin kwadago na kasar yace akwai karancin yarda da manufofin.
"Koda yake, tuni gwamnati ta riga ta fadi a yaki guda, kuma lamarin ya kasance sabo ne a tsarin fanshon, ban san wane irin kokari ne gwamnati zata yi ba wajen aiwatar da garam-bawul din, amma a yanzu babu wanda zai sake lamincewa da ra'ayin gwamnati."
Kungiyoyin ma'aikata da suka hada da malaman makarantu, da ma'aikatan sufuri, da na kiwon lafiya, sun shiga yajn aikin don nuna adawa da manufofin Macro na tsarin fanson.
Gwamnati dai ta dage cewa, tilas ne ta dauki matakan kaucewa gibi a tsarin ayyukan gwamnati.

Asalin hoton, NPF
Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya fara raba cekin kudi na inshorar jami'an da suka rasa rayukansu a bakin aiki, da kuma waɗada suka rasa wasu gaɓoɓinsu a yayin aiki.
Kudin za a raba su ne ga iyalai kimanin dubu bakwai wadanda suka rasa 'yan uwansu ko kuma suka jikkata bakin aiki ko wadanda suka rasa gaɓɓansu yayin aiki tsakanin shekarar 2012 zuwa 2020 sun haura naira biliyan 13.

Asalin hoton, NPF

Asalin hoton, NPF
Usman Baba ya ce an bayar da kuɗaɗen ne ga waɗan nan mutane domin su rike kansu, da kuma tabbatar da cewa an bayar da cikakkiyar kariya da jami'an da suka zaɓi su kare rayuwar 'yan Najeriya baki ɗaya.
Lokacin da yake tsokaci, Usman Baba ya ce kudin ba za su dawo da abin da aka rasa ba, amma za su kara kwarin gwiwa ga waɗanda ke cikin aiki wajen gudanar da aikinsu, tun da sun kwana da sani kasarsu ba za ta manta da su ba.
Baba ya kara da alkawarin samar da tsarin walwala mai kyau ga waɗanda suke aiki da waɗanda suka yi ritaya, domin ci gaba da samun waɗanda za su ci gaba da wannan aiki a cikin iyalansu

Asalin hoton, NPF

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Somaliya ta ce ta kashe masu ikirarin jihadi 50 a wani harin daukar fansa a tsakiyar kasar.
A wani sako da ta wallafa a shafinta na sada zumunta, rundunar ta ce ta kai harin ne cikin wata gona da ke yankin Shebelle, inda dakarun al-Shabab suka boye bayan harin da suka kai sansanin sojin Somliya a ranar Talata.
Rundunar ta kai harin na ranar alhamis ne da taimakon kawayenta na kasashen waje da dakarun sa kai na cikin gida.
A bara, sai da dakarun gwamnati suka kori mayakan al-Shabab daga ainihin babbar maboyarsu.
Shugaban kasar Hassan Sheik Mohamud yayin yakin neman zaben sa da ya yi nasara a bara, ya ce yakar al-Shabab na daya daga cikin manyan abubuwan da zai sa a gaba.

Asalin hoton, hk
Lawyoyi a kasar Masar sun bukaci mambonsu su shiga yajin aiki na sai baba ta gani.
Hakan ya biyo bayan hukuncin da aka yankewa wasu lauyoyi ne na zaman gida yari na shekaru biyu, bisa zarginsu da cin zarafin wasu ma'aikatan kotu.
Kungiyar lauyoyi ta kaar Masar ta bayyana matakin da cewa, shine mataki na farko da kungiyar tasu ta dauka a sakakon hukuncin da aka zartarwa lauyoyin shida a binin Mersa Matruh.
Sai dai sun ce zasu daukaka kara.

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya dauki alhakin zargin da ake yi wa dan wasansa na gaba Erling Haaland game da rashin koarin da yake wajen cin kwallo.
Haaland ya ci kwallo 27 a duka wasannin da ya buga tun bayan baro Borussia Dortmund a wannan kakar.
Amma a wasa ukun karshe da ya buga ya gaza cin kwallo sai dai Guardiola ya ce yadda ake kai masa kwallo ne ya ragu.
"Muna da salon yadda muke buga wasa, muna da ka'idojin wasanmu amma yadda muka yi wasa a wasanni biyun karshe da muka buga, ya janyo koma baya ga Haaaland," in ji Guardila.

Asalin hoton, Aj
Sama da mutane 70 ne suka mutu a ƙasar Afghanistan sakamakon matsanancin sanyi da ya addabi sassan kasar.
Tsakiyar lardin Ghor ya fuskanci yanayin sanyi mafi tsanami da ya kai kasa da maki 33 a karshen makon jiya.
Rahotanni daga kasar na cewa adadin wadanda suka mutun zai iya karuwa.
Wani jami'in hukumar hasashen yanayi na kasar ya ce wannan shine lokaci mafi tsananin sanyi da kasar ta fuskanta a shekarun baya-bayan nan.
Hukumar bada agajin gaggawa ta Afghanistan tace, shanu kusan dubu 70 ne suka mutu cikin kwanaki goman da suka gabata.
An rufe wasu titinan motan a Kabul da wasu lardunan kasar da dama, sakamakon zubar matsananciyar dusar kankara.

Asalin hoton, NRC
Hukumomi a jihar Edo da ke kudancin Najeriya, sun ce an samu nasarar ceto sauran fasinjojin da aka yi garkuwa da su a hari kan tashar jirgin ƙasa a jihar makonni biyu da suka gabata.
An kama wasu mutane bakwai haɗe da sarakuna guda biyu waɗanda ake zargi da hannu a kai harin, inda suke tsare a ofishin 'yan sanda.
A ranar 7 ga watan Janairu, wasu da ake zargin 'yan bindiga suka sace mutum 20 a tashar jirgin ƙasa ta Igueben.
Sai dai an sako mutum shida bayan kwana biyu, inda jami'an tsaro da 'yan banga suka sake kuɓutar da ƙarin wasu 12 a karshen mako a wani samame na musamman da suka kaddamar.
Garkuwa don neman kuɗin fansa dai ba sabon abu ba ne a kan hanyoyin Najeriya, inda ake nuna damuwa cewa bata gari na shirin kai hare-hare a tashar jiragen ƙasa da ke faɗin ƙasar.

Asalin hoton, AFP
An gurfanar da wata mai karbar kudi a kotun shari’ar Musulunci ta Jihar Kano, Hussaina Imam da wasu mutum 14 da suka hada da alkalai da masu rijista a gaban wata kotun majistare da ke jihar bisa zargin karkatar da zunzurutun kudi har Naira miliyan 500 da aka ware wa marayu.
A lokacin gudanar da shari’ar ranar Laraba a gaban Alkalin Kotun Mai shari’a Mustapha Sa’ad Datti, an zargi wadanda ake tuhumar da aikata laifin da ya shafi hada baki da cin amana da ma’aikatan gwamnati da kuma sata.
Mai shari'an ya ce laifin ya saɓawa sashe na 97 da 79 da 315 da 289 na kundin Penal Code.
Rahoton farko da aka fitar, ya nuna cewa wadanda ake zargin, Bashir Ali Kurawa da Saadatu Umar da Tijjani Abdullahi da Maryam Jibrin Garba da Shamsu Sani da kuma Hussaina Imam, sun aikata laifi a shekarar 2020/2021, inda Imam ta yi amfani da mukaminta na mai karɓar kudi a kotun daukaka kara ta shari'ar musulunci ta jihar Kano wajen hada baki da wasu.
Ana zargin ta da laifin buga jabun wasikun kotun Shari’a tare da sace kudi har naira miliyan ɗari hudu da tamanin da takwas da 'yan kai mallakin kotun daukaka karar shari’ar Musulunci ta jihar Kano.
Sai dai duk waɗanda ake zargi sun musanta aikata laifin da ake tuhumar su da shi, inda lauyan da ke kare su ya bukaci kotu ta bayar da belin su.

Asalin hoton, Getty Images
Gobara a sansanin sojin Armenia ta yi sanadiyyar rasuwar sojoji 15 sannan uku kuma na cikin mawuyacin hali.
Gobarar ta barke ne da sanyin safiyar Alhamis a wani sansani kusa da iyakar ƙasar da Azerbaijan.
Rahotanni sun ce wutar ta tashi ne sakamakon rashin bin ka'idoji.
Sai dai Firaminista Nikol Pashinyan, ya bayyana cewa sojojin na amfani da man fetur wajen kunna na'urar yin girki.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Afirka ta Kudu ta sanar da cewa a wata mai zuwa za ta gudanar da atisayen soji tare da ƙasashen Rasha da China a gabar tekun kasar.
Za a gudanar da atisayen na tsawon kwanaki 10 daga ranar 17 ga watan Fabrairu zuwa 27 ga watan Fabrairu a birnin Durban mai tashar jiragen ruwa da kuma Richards Bay.
Manufar ita ce musayar basira da ilimin aiki, in ji Rundunar Tsaro ta Afirka ta Kudu (SANDF).
Afirka ta Kudu na daga cikin kasashen Afirka da suka kaurace wa wani bangare na mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Kasar ta karbi shugabancin kungiyar kasashen Brics - wacce ta hada Brazil da Rasha da Indiya da kuma China - a watan da ya gabata.
Wannan dai shi ne karo na biyu da ake gudanar da irin wannan atisayen soji. An gudanar da na farko a watan Nuwamba 2019 a Cape Town.
Jami'an SANDF sama da 350 daga bangarori daban-daban ne ake sa ran za su halarci atisayen.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Crystal Palace da Manchester United sun tashi 1-1 a kwantan wasan mako na bakwai a gasar Premier da suka kara ranar Laraba a Selhurst Park.
Bruno Fernandes ne ya ci wa United kwallo daf da za su je hutu, inda Palace ta farke ta hannun Michael Olise daf da za a tashi daga wasan.
To sai dai kuma a karawar an bai wa dan wasan United, Casemiro katin gargadi, bayan da ya yiwa Wilfred Zaha keta a minti na 80.
Hakan na nufin dan kasar Brazil ya karbi katin gargadi na biyar jumulla, kenan ba zai yi wa United wasan Premier da Arsenal a Emirates ranar Lahadi ba.
''A wasan farko mun doke su ba tare da Casemiro ba, ya kamata mu kara yin hada,'' in ji dan kwallon.
Arsenal ce ta daya a teburin Premier da tazarar maki takwas tsakaninta da Manchester City ta biyu, kuma United ce kadai ta doke ta 3-1 a bana a Old Trafford.
Casemiro ya shiga wasan na Arsenal saura minti 10 a tashi daga karawar a lokacin da United ta kammala zura kwallayenta a raga.
Wasa daya kacal aka ci United a karawa 20 a dukkan fafatawa tana ta ukun teburi da maki 39 iri daya da na Manchester City ta biyu.

Asalin hoton, OTHER
Hukumar kwastam a Najeriya ta bayyana ƙwato tabar wiwi da ta kai nauyin kilo 5,124 a gaɓar tekun Legas.
Kontrolan hukumar ta kwastam a gaɓar tekun, Sani Yusuf, shi ya bayyana hakan a ranar Laraba a Legas yayin zantawa da manema labarai.
Yusuf ya ce an kwato tabar wiwi da ta kai kimanin naira miliyan 516 ne bayan samun bayanan sirri.
Ya kara da cewa an ɗauko tabar ne daga jirgin ruwa zuwa manyan motoci da nufin tafiya da su wani wuri kafin jami'ansa su dirar musu.
Ya kuma ce a ɗan tsakanin nan, tawagarsa ta kuma kwato jakukkuna 705 na shinkafar ƙasar waje mai nauyin kilo 50 wadda aka biya kuɗin shigo da shi kan naira miliyan 42 da kuma tarin tufafi.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito kontrolan na cewa tsakanin watan Janairu zuwa Disamban 2022, sun samu nasarar ƙwato kayakin da aka haramta shigo da daban-daban waɗanda kuma kuɗinsu ya kai naira biliyan 9.
Ya gargadi masu shigo da kayakin da su daina abubuwan da suke yi, inda ya ce daga yanzu ba kaya kaɗai hukumar za ta ƙwato ba, har ma da kama ke take doka domin su fuskanci hukunci.

Asalin hoton, AFP
Akalla mutum ɗaya ne ya rasa ransa sannan wasu 60 suka jikkata a wani turmutsitsi a wajen filin kwallon kafa da ke arewacin birnin Basra na ƙasar Iraqi.
Lamarin ya faru ne lokacin da dubban masoya kwallon kafa suka je filin wasa na Basra don kallon wasan karshe na gasar ƙasashen larabawa na yankin Gulf tsakanin Iraqi da Oman.
Wani jami'in lafiya ya faɗa wa Kamfanin Dillancin Labaran Iraqi cewa sauran waɗanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.
Hotunan bidiyo sun nuna mutane da dama kwance basa motsi a kasa.
Gasar kwallon kafar ta ƙasashen larabawa na yankin Gulf, shi ne gasar yanki na farko da aka gudanar a Iraqi sama da gomman shekaru.
An yi hakan ne domin dawo da kimar ƙasar bayan rikice-rikice na siyasa na tsawon shekaru.

Asalin hoton, Laolu Akande
Majalisar zartaswa ta tarayya a ranar Laraba, ta amince da shawarar da ma'aikatar ayyuka da gidaje ta bayar na ganin kamfanin mai na ƙasa NNPC ya zuba kuɗi naira tiriliyan 1.9 don aikin sake gyara hanyoyi 44 a faɗin Najeriya.
Mataimaki na musamman kan harkokin ƴaɗa labaru a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Laolu Akande, shi ya sanar da haka bayan taron da mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Akande ya ce kudaden da ake sa ran kashewa sun kasance don ci gaba da aiwatar da tsarin bunkasa ababen more rayuwa ne na tituna da kuma gyara tsarin ba da harajin zuba jari na gwamnatin tarayya, kashi na biyu na NNPC Ltd da sauran rassansa.
Ya ce majalisar ta kuma amince da masu ba da kwangilar gina tituna guda tara a ƙarkashin tsarin gwaji na shirin bunƙasa manyan tituna da gudanar da ayyukansu bayan bayar da cikakken takardar shaidar bin ka’idojin kasuwanci da hukumar kula da hanyoyin samar da ababen more rayuwa ta yi na tsawon shekaru 25.
Aikin hanyoyi da aka amince a matakin farko sun hada da hanyar Benin-Asaba da Abuja-Lokoja-Onitsha-Owerri-Aba-Shagamu-a Benin da Abuja-Keffi-Akwanga-Lafia da Makurdi da hanyar Kano-Maiduguri da hanyar Enugu-Port Harcourt da Legas-Ota-Abeokuta da kuma Legas-Badagry zuwa Seme.

Asalin hoton, KFC
Afirka ta Kudu na iya fuskantar ƙarancin kaji sakamakon matsalar wutar lantarki da take fama da shi wadda kuma ke shafar kajin da ake yankawa, a cewar kungiyar masu kiwon kaji ta ƙasar.
Kungiyar ta ce rashin wutar lantarki ya sanya ta rage yawan kaji da take yankawa saboda mayanka ba sa iya adana su saboda ƙarancin wuta.
Kafofin ƴaɗa labarai na cikin gida sun ruwaito kungiyar na cewa ta matsalar ta wutar lantarki ta kai ta ga kasa yanka kaji kusan miliyan 10 a makonni da suka gabata.
Tasirin ƙarancin wutar lantarkin har ya fara shafar kantunan sayar da abinci irinsu KFC, inda ake kyautata zaton cewa lamarin zai iya taɓarɓarewa.
Hakan na zuwa ne bayan wani gargadi na cewa lamarin zai iya ɗaukar tsawon lokaci wadda kuma zai shafi harkokin hada-hadar kasuwanni.

Asalin hoton, AFP
Jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun gano wagegen rami cike da gawarwaki a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.
Gano wagegen ramin na zuwa ne bayan jerin hare-hare da kungiyoyi masu rike da makamai ke kai wa a yankin Ituri.
Wani mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya, Farhan Haq, ya ce sun gano gawarwakin mutane 42 a kauyen Nyamamba haɗe da mata da ƙananan yara, da kuma wasu maza bakwai a kauyen Mbogi.
Jami'an wanzar da zaman lafiyar sun kaddamar da shirin kai samame a yankin bayan samun rahotannin kai hare-hare da mayakan Codeco ke yi.
Yawancin mayakan sun fito ne daga al'ummomin Lendu waɗanda galibi manoma ne da kuma suka daɗe suna rikici da makiyaya na kabilar Hema.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin jihar Edo, ta ce ta kama sarakun guda biyu tare da wasu mutum biyar waɗanda ake zargi da hannu a garkuwa da fasinjoji 20 a hari kan tashar jirgin ƙasa a jihar ranar 7 ga watan Janairu.
Kwamishinan sadarwa da wayar da kai a jihar, Chris Nehikhare, shi ya bayyana hakan jiya a Benin yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan fitowa taron majalisar zartaswa.
Ya ce jami'an tsrao sun samu nasarar kuɓutar da mutum biyu da suka rage a hannun masu garkuwa da mutanen.
A ranar 7 ga watan Janairu ne, wasu da ake zargin 'yan bindiga suka kai hari tashar jirgin ƙasa a jihar tare da sace mutum 20.