Yan bindiga sun kai hari kan ɗan takarar Jam'iyyar APGA a Ebonyi

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu

  1. Sai da safe

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra’ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.

  2. Amurka za ta bai wa Ukraine makamai masu cin dogon zango

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka za ta bai wa Ukraine makaman roka masu cin dogon zango a matsayin wani bangare na tallafin soji da ya kai dala biliyan biyu da ɗuriya.

    Bayan rokokin akwai kuma na'urorin daƙile hare-hare ta sama da kuma tankunan yaki da motocin sulke.

    Mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Pentagon ya ce idan aka haɗa da horaswa, toh makaman za su taimaka wa Ukraine wajan kwato yankunan da aka mamaye.

  3. Yan bindiga sun kai hari kan ɗan takarar Jam'iyyar APGA a Ebonyi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga Jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya na cewa ƴan bindiga sun kai hari ga ɗan takarar gwamnan jihar na Jam'iyyar APGA Benard Odoh, inda har suka kashe direban.

    Gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne tun a jiya Alhamis da dare a Okpoto da ke Ƙaramar Hukumar Ishielu ta Jihar Ebonyi.

    Rahotanni sun ce ƴan bindigan sun je wurin ne cikin wata mota ƙirar Sienna ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47.

    Gidan talabijin ɗin ya ce ɗan takarar ya tabbatar musu da faruwar lamarin bayan ya aika musu da saƙo ta murya.

  4. Shugaban Habasha ya tattauna da jagororin yankin Tigray

    .

    Asalin hoton, Ethiopian News Agency

    Firaiministan Habasha Abiy Ahmed ya tattauna da shugabannin yankin Tigray a karon farko tun bayan da ɓangarorin biyu suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta watanni uku da suka gabata.

    Wasu hotuna waɗanda kafar watsa labarai ta Habasha ta saki sun nuna Mista Ahmed da wasu jami'an gwamnati a zaune tare da sauran manyan shugabannin Tigray, ciki har da kwamandan dakarun na Tigray Janar Tadesse Worede.

    An bayar da rahoton cewa sun tattauna kan batun ci gaban da aka samu wurin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma wasu matsalolin da ake buƙatar ƙara dubawa.

    Yarjejeniyar tsagaita wutan ta kawo ƙarshen yaƙin basasan da aka shafe shekaru biyu ana yi da ya jefa ƙasar cikin tasku.

  5. EFCC ta kama ƴar fim a Legas kan zargin liƙa sabbin kuɗi a wurin biki

    ..

    Asalin hoton, EFCC

    Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC reshen Jihar Legas ta soma gudanar da bincike kan Oluwadarasimi Omoseyin kan zargin lalata darajar sabbin kuɗin Najeriya.

    Omoseyin wadda ƴar fim ce kuma mai sana'ar gyaran jiki an kama ta ne tun a ranar Laraba bayan wasu bayanan sirri da hukumomin yaƙi da cin hanci suka samu.

    An kama matashiyar ƴar shekara 31 bayan an ga wani bidiyo yana yawo a shafukan sada zumunta wanda aka ga tana liƙa kuɗi kuma tana tattake su a wurin wani biki, kamar yadda aka yi zargi.

    Hukumomi sun ce cikin abubuwan da aka kama ta da su har da mota ƙirar Range Rover da waya Iphone.

    Haka kuma hukumar ta EFCC ta bayyana cewa za a gurfanar da ita a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

  6. An ceto mutum 24 da rushewar gini ya rutsa da su a Abuja

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin bayar da agaji a Najeriya sun ce aƙalla mutum 24 aka ceto daga wani gini da ya rushe a Abuja.

    Hukumoimin sun tabbatar da cewa akwai mutum uku waɗanda suka rasu sakamakon munanan raunukan da suka samu.

    Ginin mai hawa uku wanda kuma aka yi shi da tsarin ginin ƙarƙashin ƙasa, ya rushe ne a ranar Alhamis a lokacin da ake ci gaba da aikin gina shi.

    Babu tabbaci kan adadin mutum nawa rushewar ginin ta rutsa da su amma akasarinsu leburori ne.

  7. Shugaban NNPP a Gombe ya koma APC

    ..

    Asalin hoton, Gombe State Government

    Shugaban Jam'iyyar NNPP reshen Jihar Gombe Abdullahi Maikano Umar ya yi murabus a matsayin shugaban jam'iyyar inda ya sauya sheƙa zuwa APC.

    A wata sanarwa ɗauke da sa hannun tsohon shugaban, ya bayyana cewa rashin manufa ta siyasa ta ɗan takarar jam'iyyar ta NNPP a jihar ne ya sa ya fita daga jam'iyyar domin a cewarsa, bai ga alamun yadda ɗan takarar jam'iyyar Khamisu Mailantaerki zai ciyar da jihar Gombe gaba ba.

    "Ba zan zauna wurin da ƙarerayi ne ke zama a kan gaba ba a wurin yaƙin neman zaɓe a maimakon a rinƙa magana a kan hanyoyin ci gaba na gwamnati," in ji Abdullahi Maikano.

    Haka kuma an ga hoton tsohon shugaban na NNPP da Gwamnan Jihar Gombe Inuwa Yahaya.

    ..

    Asalin hoton, Abdullahi Maikano

  8. Ƴan ci-rani takwas sun mutu yayin ƙoƙarin tsallaka tekun Bahar Rum

    Dis migrants dem end up inside water, as dem try to enter Italy inside boat wey dem make with wood

    Asalin hoton, Getty Images

    An gano gawawarkin 'yan ci-rani takwas da suka mutu yayin da suke kokarin ketara tekun Bahar Rum a wani aikin ceto da jami'an tsaron gabar ruwan Italiya suka yi a tsibirin Lampedusa.

    A cikin wadanda suka rasa rayukansu har da wata mata mai juna biyu.

    An kuma ceto wasu 'yan ci-rani 42 da ke cikin jirgin ruwan, sai dai wadanda suka tsira sun ce wasu mutane biyu ciki har da wani jariri sun rasa rayukansu a cikin jirgin yayin da suka taso daga Tunisia.

  9. 'Mun yi hannun riga da tsarin canjin kudi na gwamnan CBN da wadanda suka zagaye Shugaba Buhari'

    Gwamnan Kano Abdullahi Umar Gandulje

    Asalin hoton, FACEBOOK / KANO STATE GOVT

    Bayanan hoto, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Gandulje

    Gwamnonin Najeriya karkashin jam'iyyar APC mai mulin kasar sun bayyana wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa manufar gwamantinsa ta sauyin fasalin takardun naira 200 da 500 da kuma 1,000 za ta haifar da tarin matsaloli.

    Gwamnonin sun ce wannan ne yasa suka kuduri aniyar komawa jihohinsu domin fadakar da al'umominsu cewa jam'iyarsu ta APC ba ta da hannu ko kadan wajen fito da wannan manufar.

    Bayan wata ganawa da gwamnonin suka yi da shugaban kasar, gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya shaida wa BBC cewa:

    "Wannan ba ajandar APC ba ce, ajanda ce ta wadanda suka zagaye shugaban kasa, da kuma shi gwamnan babban bankin Najeriya wanda ka san ya nemi ya zama shugaban kasa amma abin ya lalace. Shi yasa suke son ko dai zaben nan ba a yi shi ba, ko kuma wata jam'iyyar ta lashe shi."

    Kan ko gwamnonin za su yi hannu riga da shugaban kasa kan wannan manufar, sai Gwamna Ganduje ya ce:

    "A'a, mu muna hannun riga da wannan tsari na canjin kudi na gwamnan babban banki da kuma wadanda suka zagaye shugaban kasa."

  10. Yadda aka kashe alƙali a kotu a jihar Imo

    ...

    Asalin hoton, EMPEROR IWUALA

    Bayanan hoto, ...

    Ƴan bindiga sun kashe wani alƙali mai suna Nnaemeka Ugboma, wanda shi ne ke jagorantar wata ƙaramar kotu a ƙaramar hukumar Oguta a jihar Imo.

    Bayanai sun ce an harbe alƙalin ne a bakin aiki, wani abu da ya sanya mahalarta zaman kotun suka tsere.

    Wani shaida ya faɗa wa BBC cewar waɗanda suka aiwatar da kisan sun isa kotun ne a kan babur.

    Ya ce "sun shigo kotun, suka ja shi waje, suka harbe shi sannan suka gudu."

    Ya ce a lokacin ne mutane suka tsere domin gudun kada abin ya rutsa da su.

    Shugabar ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen jihar Imo, Ugochukwu Allinor ta tabbatar da kisan alƙalin.

    Ta kuma ce ƙungiyar na gudanar da bincike domin sanin gaskiyar lamarin, kafin su fitar da bayani.

    Sai dai mai magana da yawun rundunar ƴan sanda a jihar, Henry Okoye bai amsa kiran wayar da kuma sakonnin waya da aka tura masa ba domin neman ƙarin bayani.

  11. Hukumar yaki da aikata miyagun laifuka ta musanta cewa tana binciken Tinubu

    Bola Ahmed Tinubu, APC presidential candidate

    Asalin hoton, KSGV

    Hukumar yaki da masu aikata miyagun laifuka a Birtaniya ta ce wasiku biyu da suka zargi 'yan takarar mukamin shugaban kasa a Najeriya da jam'iyyun siyasar kasar da aikata ba dai-dai ba, wadanda aka rika yadawa a shafukan sada zumunta na jabu ne.

    Dubban mutane ne sun karanta wasikun da aka wallafa a Twitter da ake zargin hukumar ta NCA ce ta wallafa su.

    Wasika ta farko da ta bayyana a karshen watan da ya gabata amsa ce ta bogi ga wani bincike da ake yi kan zargin da ake yi wa dan takarar shugaban kasa na jamiyyar APC mai mulkin kasar Bola Ahmed Tinubu da almundahana.

    Ita kuwa wasika ta biyu ta yi ikirarin cewa hukumar ta NCA na binciken jam'iyyar hammaya ta Labour kan zargin rubuta wasikar ta farko ta bogi.

  12. Fafaroma Francis ya sauka a Sudan ta Kudu

    Pope Francis has arrived at the airport in South Sudan's capital, Juba

    Fafaroma Francis ya sauka a filin jirgin saman Juba babban birnin Sudan ta Kudu - kasa ta biyu ta ziyarar da ya kai a nahiyar Afirka.

    Dubban jama'a sun hallara domin yi masa maraba.

    Pope Francis has arrived at the airport in South Sudan's capital, Juba

    Ya isa wannan kasar ce da rikici da yaki ya daidaita domin ya mika sakon zaman lumana, kuma akwai wasu shugabannin addinin Kirista, ciki har da shugaban darikar Anglican na Ingila Archbishop na Canterbury Justin Welby.

    Pope Francis has arrived at the airport in South Sudan's capital, Juba
  13. Mutumin da ya kitsa kashe Sarauniya Elizabeth ya amsa laifin cin amanar kasa

    Jaswant Singh Chail appeared on a video link from Broadmoor Hospital

    Asalin hoton, JULIA QUENZLER

    Bayanan hoto, Zanen da aka yi na Jaswant Singh Chail yayin wani zaman kotu da aka yi

    Wani mutum da ya je Fadar Windsor Castle dauke da kwari da baka kuma ya shaida wa dan da sandan da ke tsaron ginin "Na zo nan domin kashe Sarauniya ne", ya amsa laifin cin amanar kasa.

    An kama Jaswant Singh Chail, daga garin Hampshire ne ranar Kirsimetin 2021 yayin da marigayiya Sarauniya Elizabeth ke zama a Fadar ta Windsor saboda annobar koronar da ake fama da ita.

    Yayin da aka gabatar da shi a gaban alkali a kotun Old Bailey, Chail mai shekara 21 ya amsa dukkan tuhume-tuhume ukun da ake masa.

    Chail's crossbow was found to be comparable to a powerful air rifle with the potential to cause fatal injury

    Asalin hoton, CPS

    Bayanan hoto, Wannan ne kwari da bakan da aka ga Chail yake dauke da su

    Shi ne mutum na farko da aka yanke wa hukuncin ci amanar kasa a Birtaniya tun 1981. Chail ya kuma yarda cewa ya aikata laifukan furta cewa zai yi kisa, da kuma samunsa dauke da makamin da ka iya kisa.

    A halin yanzu ana kulawa da shi a asibitin Broadmoor, wurin da aka hada shi da zaman kotun ta intanet yayin zaman da ya amasa laifukan nasa uku.

    Dan sandan da ya fara ganinsa a Fadar ta Windsor ya umarce shi d aya durkusa, kuma ya dra hannayensa bisa kansa kuma Chail ya bi umarnin da ya ba shi.

    Sai dai ya sake cewa: "Na iso nan domin kashe Sarauniya ne." An kuma sai wata wasika da ya rubuta a cikin kayan da yake sanye da su, wadda a ciki ya ce:

    "Don Allah kar a cire min kayan da nake sanye da su, bana kuma son a binciki gawata ta hanyar fede ta, ba na bukatar a kyafe gawata, na gode kuma na yi nadama."

    Jaswant Singh Chail climbed into the grounds using a nylon rope ladder

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Fadar Windsor Castle

    Cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Snapchat mintuna kadan kafin ya shiga Fadar ta Windsor, Chail ya ce:

    "Ina nadamar abin da na aikata da abin da zan aikata. Zan yi kokarin kashe Elizabeth, Sarauniyar Gdan Sarauta. Wannan ramuwar gayya ce ga wadanda suka rasa rayukansu a kisan kiyashin Jallianwala Bagh na 1919. Wannan kuma ramuwar gayya ce ga dukkan wadanda aka kashe ko aka tozartar ko aka nuna musu bambanci saboda launin fatarsu."

  14. An raunata yara a fadar shugaban Saliyo

    President Julius Maada Bio and the First Lady were in attendance

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaba Julius Maada Bio da mai dakinsa na wurin bikin

    An raunata wasu yara da suka halarci wani biki da aka yi a fadar shugaban Saliyo, bayan da wani mariki bayar da kariya ya karye yayin da Shugaba Julius Maada Bio da mai daknsa ke raba wa matasan kunzugun al'ada kyauta.

    Bidiyon da ake yadawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda jama'a masu yawa ke ficewa daga filin wasan da aka yi bikin a birnin Bo, inda ana iya ganin wasu mutane dauke da wadanda suka sami raunuka, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

    Shugaba Mada Bio ya aika da sako ta shafinsa na Tiwita ga wadanda suka raunata:

    "Ina cike da tausayi ga dukkan yaran da wannan lamari ya rutsa da su tare da iyalan yaran da suka sami raunuka a wannan abin takaicin da ya faru a filin wasa na Bo a yau."

    Kawo yanzu ba a san yawan yaran da suka sami raunuka ba. Hadarin ya auku ne yayin da wani gajeren karfe mai kare wani bangare na filin wasan da ke sama ya balle, kamar yadda wata sanarwar da kakakin gwamnatin kasar ya fitar ke cewa.

  15. Daliban makaranta sun kai wa 'yan sanda hari bayan kashe abokin karatunsu

    Wasu dalibai a lardin Free State na Afirka ta Kudu sun yi wata tarzoma a ranar Alhamis bayan da labarin mutuwar wani dan makarantarsu, lamarin da yasa har suka juya wata motar 'yan sanda har suka jrikitar da ita a gefenta.

    Wani rahoton jaridar intanet mai suna Times Live, ya nuna cewa dan makarantar ya kashe kansa ne a sanadiyyar muzgunawar da wani malami ya rika yi masa.

    'Yan sandan yankin sun sanar cewa, "Dalibin ya bar wata wasika da ke cewa malamin ne yayi sanadin kashe kansa da yayi."

    Bayyanar labarin mutuwar dalibin ya sa 'yan makarantar "su tunzura kuma suka fara lalata kayayyakin makarantar", kamar yadda jami'in 'yan sanda Warrant Officer Peter Mabizela ya sanar.

    Daga nan ne dalibai daga makarantun da ke kusa suka tarua makarantar sakandare ta Tlotlisong, inda suka yi garkuwa da wasu 'yan sanda biyu da malaman makarantar cikin wani daki.

    Daliban sun kuma kai wa motar 'yan sandan hari, inda suka juya ta zuwa gefenta. Sai dai aka tura karin jami'an 'yan sanda sannan aka kwantar da tarzomar daliban.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. An yanke wa tsohon dan sanda hukuncin kisan wani lauya da wasu mutum biyu a Kenya

    Human rights lawyer Willie Kimani was murdered in 2016

    Asalin hoton, AFP

    Wata kotu a Kenya ta yanke wa wani tohon dan sanda hukuncin kisa saboda kisan wani mai lauya fafutukar kare hakkin dan Adam da wasu mutum biyu kimanin shekara shida ta gabata.

    Sai dai Kenya ba ta aiwatar da hukuncin kisa, duk da cewa dokar kasar ta bukaci a yi haka.

    Akwai kuma wasu 'yan sanda biyu da wani farar hula da aka yanke wa hukuncin daurin shekara 15 zuwa 39 a kurkku a dalilin kisan lauyan mai suna Willie Kimani, da wani mutumin da kuma direban tasi a watan Yunin 2016.

    A bara ne kotun ta same su da laifuka uku-uku ciki har da na kisan kai.

    Sai dai duka mutanen na iya daukaka kara cikin kwanaki 14.

  17. Gwamnonin APC sun ki amincewa da daina sauya takardun naira a ranar 10 ga Fabrairu

    Gwamna Bagudu na jihar Kebbi

    Asalin hoton, BAGUDU/TWITTER

    Gwamnonin jihohin Najeriya da aka zaba a karkashin jam'iyya mai mulkin kasar ta APC sun ki amicewa da wa'adin 10 ga watan Fabrairu da babban bankin Najeriya ya shata wa al'ummar kasar na su kamala sauya tsofaffin takardun naira na N1000, N500 and N200 da sababbin da ya fitar.

    Gwamnonin sun ce bayanan da ke isa garesu daga al'umominsu sun tabbatar musu cewa al'umomin na shan bakar wahala cikin 'yan kwanakin da suka gabata yayin da suke kokarin sauya takardun kudin, saboda lokacin da bankin ya bayar bai zo a lokacin da ya dace ba da kuma dalilin illar da matakin ke yi wa tattalin arzikin kasar.

    Wannan ne yasa suka yanke shawarar ganawa da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da misalin karfe 10 na safiyar Juma'a.

    Cikin jihohi 36 na Najeriya, jam'iyyar APC na iko da jihohi 21 ne.

    Gabanin yanke wannan hukuncin ganawa, gwamnonin sun zabi gwamna Babajide Sanwo-Olu (Lagos) da Nasir El-Rufai (Kaduna) da Mai Mala Buni (Yobe) da kuma Dapo Abiodun (Ogun) domin su gana da gwamnan babban bankin Godwin Emefiele, kuma yayin tattaunawar da suka yi, sun sanar da shi rashin gamsuwarsu da "garaje da hanzarin" da ake nunawa na aiwatar da sauyin takardun kudin.

    Sun kuma sanar da Mista Emefiele cewa babban bankin Najeriya ya gaza a aikin da aka ba shi na sauya takardun kudin ganin yadda 'yan Najeriya ke fafutukar karbar takardun kudinsu da suka ajiye da kawunansu a bankunan kasar.

  18. Budewa!

    Ga masu bibiyar BBC Hausa a intanet da shafukan sada zumunta, Sani Aliyu ke muku lale marhabin!

    Ni ne zan jagoranci aiko muku da labarai da rahotanni ta wadannan kafafen a tsawon wannan rana ta Juma'a. Sai ku kasance tare da BBC Hausa a nan BBC Hausa dot com, ko a BBC Hausa Facebook da kuma a Twitter.