Majinyata sun maƙale yayin da ake harbe-harbe a bakin asibitocin Gaza

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Ahmad Tijjani Bawage, Mukhtar Adamu Bawa and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki Abdullahi bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. An kai hari kan asibitoci uku a Gaza

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an Falasɗinawa sun ce hare-haren Isra'ila sun faɗa kan asibitoci uku da makaranta guda a Gaza, tare da kashe fiye da mutum 20.

    Daraktan babban asibitin Al-Shifa da ke Gaza, ya zargi Irsa'ila da ƙaddamar da yaƙi kan asibitocin.

    Ƙungiyar Agaji da Red Cross ya yi gargadin cewa asibitocin Gaza sun 'kai maƙura'.

    Rahotonni sun ce tankokin yaƙin Isra'ila sun zagaye asibitin al-Shifa, yayin da ƙungiyar agajin Falasɗinawa ta Red Crescent ta ce masu harbin sari-ka-noƙen Isra'ila suka buɗe wuta kan asibitin Al-Qudus, tare da kashe mutum guda.

    Mai magana da yawun sojojin Isra'ila ya ce sojojin ƙasar ba su buɗe wuta a asibitoci ba, amma idan sun ga mayaƙan Hamas a ciki, sai sun kashe su.

    Jami'an lafiya a Gaza sun ce kawo yanzu fiye da mutum 11 ne suka mutu a Gaza sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kai wa Hamas.

  3. Biden zai gana da Xi Jinping a makon gobe

    Shugaban Amurka Joe Biden zai gana da takwaransa na Chaina, Xi Jinping a birnin San Fransisco cikin mako mai zuwa.

    Shugabannin biyu za su gana ne a yayin taron haɗin kan raya Tattalin Arzikin ƙasashen Asiya da yankin Pacific watau APEC.

    Wannan shi ne karon farko da shugabannin biyu za su gana tun bayan zaben Mista Biden a matsayin shugaban kasar Amurka.

    Ana sa ran za su tabo batutuwan inganta dangantakar ƙasashen biyu.

  4. 'An katse ruwan sha da wutar lantarki a asibitin Gaza'

    .

    Asalin hoton, Reuters

    A yayin da muka kawo muku rahotonnin abubuwan fashewa a ciki ko kusa da asibitoci a Gaza a daidai lokacin da sojojin Isra'ila ke tsananta hare-hare a yankin.

    Ƙungiyar agajin Falasɗinawa ta Red Crescent ta ce an yanke wutar lantarki da ruwan sha da hanyoyin sadarwar intanet a asibitin 'Indonesian Hospital' da ke birnin Gaza.

    Mai magana da yawun ƙungiyar, Nebal Farsakh, ta ce likitoci da masu tiyata na amfani da fitilu domin gudanar da tiyatar ceton rai, sakamakon katsewar wutar lantarki.

    “Suna aiki a wani yanayin da babu wani ma'aikacin lafiya a duniya da zai iya yin aiki a yanayin," kamar yadda ta shaida wa BBC.

    Ta kuma cewa duka ayyuka za su iya 'tsayawa' a asibitin nan da sa'o'i masu zuwa sakamakon halin da ake ciki.

  5. James Maddison ya fice daga tawagar Ingila saboda rauni

  6. Kotu ta hana NLC da TUC shiga yajin aiki

    s

    Asalin hoton, NLC/TUC

    Kotun ɗa'ar ma'aikata ta dakatar da gamayyar kungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC daga shiga yajin aikin da suka yi niyyar shiga a ranar Talata 14 ga watan Nuwamba.

    A ranar Juma'a da maraice ne kotun ta bayar da umarnin dakatar da ƙungiyoyin biyu daga fara yajin aikin da suka shirya gudanarwa cikin mako mai zuwa.

    Alƙalin kotun, mai shari'a Benedict Kanyip ne ya yanke hukuncin dakatar da yajin aikin bayan ƙarar da gwamnatin Najeriya da ministan shari'ar ƙasar suka shigar gaban kotun suna neman kotun ta hana ƙungiyoyin shiga yajin aikin, saboda hakan zai iya jefa 'yan ƙasar cikin ƙarin wahala.

    Lauyan masu gabatar da ƙarar Barista Tijani Gazali ya ce matsawar ba a dakatar da ƙungiyoyin daga shiga yajin aikin ba, za a iya samun tayar da hargitsi tare da kawu ruɗani a fadin ƙasar.

    Yayin da yake hukuncin, alƙalin kotun ya ce kotun na da hurumin shga tsakani domin hana duk wani abu da ka iya tayar da hankula ƙasar.

    Mai shari'a Kanyip ya yi amfani da sahe na 17 da 19 na kundin dokokin kotun wajen dakatar da yajin aikin.

  7. Ribadu ya tabbatar da samar da tsaro a lokacin zaɓen gwamna a jihohi uku

    n

    Asalin hoton, X/Ribadu

    Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya tabbatar da samun ingantaccen tsaro ga mazauna Kogi da Beyalsa da kuma Imo a lokacin zaɓen gwamnan da za a gudanar ranar Asabar jihohin

    Ribado ya gargaɗi 'yan siyasa kan ƙoƙarin tayar da hargitsi, tare da kira ga jami'an tsaro da su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa a lokacin aikin.

    Cikin wata sanarwar da ofishinsa ya fitar, ya ce gwamnatin tarayya ta kammala duk wani shiri da ake buƙata don gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana.

    Sanarwar ta ƙara da gargaɗin cewa za a samar da tawagar masu sanya idanu a zaɓen domin tattaro bayanan hujjojin tayar da hargitsi ko take dokokin zaɓen.

    Ribadu ya sha alwashin ɗaukar tsattsauran mataki ga duk wanda aka samu da tayar da yamutsi, ko keta doka a lokacin zaɓen.

    Ya kuma yi kira ga masu kaɗa ƙuri'a a jihohin uku da su yi dafifi wajen fitowa domin kaɗa ƙuri'unsu, inda ya tabbatar musu da cikakken tsaro.

  8. Zaɓen Kogi: Za mu taka wa masu aniyar tayar da hargitsi birki

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Yayin da ake gudanar da zaɓen gwamnan jihar Kogi a ranar Asabar, DIG Habu Sani ya yi mana ƙarin bayani game da manyan matakan tsaron da aka ɗauka domin tabbatar da cewa an yi zaɓen ba tare da wata matsala ba.

  9. Ɗan wasan Leverkusen da ya zaƙu ya fara buga wa Najeriya wasa

  10. Ana jin ƙarar harbe-harbe da ababen fashewa a kusa da asibitin Al-Shifa

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Tankokin yaƙin Isra'ila sun tunkari asibitin Al-Shifa daga ɓangaren arewazi da kudanci

    Asibitin ya fuskanci hare-hare ta sama da makaman atilare da harbe-harben bindiga.

    An jin ƙarar abubuwan fashewa da harsasai, ga kuma gawarwaki masu yawa da ake kawo su asibitin a motoci da amalanke ko kekunan doki.

    A cikin asibitin akwai dubban mutanen da suka jikkata, inda da yawa ke cikin mayuwacin hali sakamakon munanan raunukan da suka ji, waɗanda ba za su iya barin asibitin ba, saboda girman raunin da suke da shi.

    Mutane da dama na zaune a asibitin ne domin kula da 'yan uwansu, duk kuwa da mummunan yanayin da ake ciki.

    Akwai ƙarancin man fetur da magunguna, kuma ana ganin tankokin yaƙin Isra'ila na tunkarar asibitin.

    Dubban mutane sun fice daga asibitin domin tafiya wuraren da suke tunanin za su samu kariya, to sai dai babu wani wuri da za a iya cewa akwai kariya a duka faɗin Gaza.

  11. Mutum biyu sun jikkata yayin da Hamas ta harba rokoki birnin Tel Aviv

    Tel aviv attack

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotonni daga birnin Tel Aviv na Isra'ila na cewa wasu mata biyu sun jikkata sakamakon wasu makaman roka da Hamas ta harba zuwa birnin.

    Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato ma'aikatan lafiya na cewa “An samu harin makaman roka da misalin ƙarfe 2;00 a birnin Tel Aviv, inda makaman suka faɗa wurare biyu a birnin''.

    Kungiyar Hamas ta ce hare-haren ramuwar gayya ne kan kisan fararen hula da ake yi a Gaza.

    Sojojin Isra'ila sun ce tun ranar 7 ga watan Oktoba an harba makamai kusan 9,500 zuwa cikin Isra'ila, da suka haɗar da rokoki da jirage marasa matuƙa daga Gaza da wasu sassa.

    Sojojin sun ce kashi 12 na makaman da aka harba cikin Isra'ila na faɗuwa a cikin yankin Falasɗinawa.

  12. Mazauna Lokoja sun koka kan tsadar rayuwa gabanin zaɓen gwamna

    Mazauna Lokoja, babban birnin jihar Kogi sun koka kan rashin ababen more rayuwa da matsin rayuwa.

    Sun ce fatansu shi ne duk wanda ya yi nasara a zaɓen gwamnan jihar da za a yi a ranar Asabar zai ɗauki matakin magance musu matsalolin da ke ci musu tuwo a kwarya.

    Ga rahoton Raliya Zubairu daga Lokoja.

    Bayanan sautiLatsa sama don sauraron rahoton
  13. Za a gurfanar da ɗan uwan Rashford a kotu

  14. Tinubu ya yi alhini kan mutuwar mace Manjo Janar ta farko a Najeriya

    Shugaba Bola Tinubu ya bayyana mutuwar Aderonke Kale, mace ta farko da ta fara kai wa mukamin Manjo Janar a rundunar sojin Najeriya, a matsayin asara mai zafi ga kasar.

    Kale, wadda kuma ita ce mace da ta fara zama kwamandar rundunar sojoji likitoci, ta rasu ne ranar Alhamis tana da shekara 84.

    A cikin wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar, Bola Tinubu ya mika sakon ta'aziyya ga 'ya'ya da dangin Janar Kale mai ritaya da kuma rundunar sojin Najeriya da kungiyoyin likitoci na Najeriya kan rasuwar daya daga cikinsu.

    Tinubu ya ce a matsayinta na mace ta farko a fagen da ta yi zarra, marigayiyar Manjo Janar din ”mai dumbin kwarin gwiwa da kwarewar aiki da kwazo da juriya irinta matan Najeriya”.

    Shugaba Tinubu ya yi addu'ar neman jin kai ga marigayiyar, kuma ya yi fatan 'yan'uwa da dangi za su yi hakuri kan wannan rashi da suka yi.

  15. Shugaban ƙaramar hukumar Lokoja a jihar Kogi ya rasu

    Shugaban ƙaramar hukumar Lokoja a jihar Kogi, Muhammed Danasabe ya rasu.

    Danasabe ya rasu ne da safiyar ranar Juma'a, a wani asibitin Lokoja bayan wata gajeriyar rashin lafiya.

    Mutuwar tasa, na zuwa ne sa’o’i 24 kafin gudanar da zaɓen gwamna a jihar.

    Jaridar Vanguard a Najeriya ta ambato wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar APC a Lokoja, Talba Lakwaja, da ke tabbatar da mutuwar shugaban ƙaramar hukumar.

    “Wannan shi ne don sanar wa da jama’a cewa za a binne gawar shugaban ƙaramar hukumar Lokoja, Hon. Mohammed Dasebe Mohammed a maƙabartar Anguwan Kura da karfe 2 na rana bayan sallar Juma'a.

    "Za a ɗauki gawar tasa daga gidan danginsa zuwa babban masallacin Lokoja da karfe 1:30 na rana,” in ji sanarwar.

  16. Labarai da dumi-dumi, Sama da mutum 11,000 aka kashe a Gaza - ma'aikatar lafiyar Hamas

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce adadin wadanda suka mutu a yaƙin da ake yi ya kai 11,078.

    Wannan ya haɗa da yara 4,506 da mata sama da 3,000 kamar yadda ma’aikatar ta wallafa a shafin Telegram.

    Sama da mutum 27,000 ne suka jikkata, in ji sanarwar.

    Idan aka kwatanta, Majaliasar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutum 5,400 ne aka kashe a Gaza a duk fadan da Isra'ila ta yi a baya da Hamas tun bayan da ta karɓe ikon yankin a shekara ta 2007.

    A baya dai Amurka da Isra'ila sun ce ya kamata a yi taka-tsantsan da alƙaluman ma'aikatar da Hamas ke gudanarwa, amma a baya Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce alkaluman na da sahihanci.

  17. Tinubu ya gargaɗi jami’o’i kan ƙarin ƙudin makaranta

    ...

    Asalin hoton, Aiwaju Bola Ahmed Tinubu/Facebook

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gargadi mahukuntan jami’o’in gwamnati da su guji kara kudin makaranta ba bisa ka’ida ba.

    Tinubu wanda ya samu wakilcin karamin ministan ilimi, Dakta Yusuf Sununu, ya ce matakin na hana samun damar zuwa manyan makarantu, musamman ga matasa marasa galihu a kasar.

    Da yake magana a ranar Alhamis a garin Uyo yayin taron kammala karatu na jami’ar Uyo ta jihar Akwa Ibom, shugaban ya ce ƙarin kudin makaranta ba bisa ka’ida ba na yin illa ga ci gaba da bunkasar makarantun gaba da sakandare.

    • Dalibai: 'Ba za mu lamunci karin kudin makaranta a jami'oi ba'
    • Komawa makarantar kan zo da karin kudin makaranta da kashe kudi makudai
  18. Sir Jim Ratcliffe na daf da sayen hannun jari a Man United

  19. Yadda ake jana'izar Falasɗinawan da suka mutu a samamen Isra'ila bayan rikicin Jenin

    A Yamma da Gaɓar Kogin Jordan, mutane da dama sun halarci jana'izar Falasɗinawa 11 da aka kashe a wani samame da Isra'ila ta kai a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin.

    Ma'aikatar lafiya ta yankin - daban da ta Gaza da Hamas ke gudanarwa - ta fada jiya cewa mutane 14 ne aka kashe gaba daya.

    Ma'aikatar ta ƙara da cewa wasu 20 sun jikkata a harin.

    Wannan dai na ɗaya daga cikin mafi munin lamarin da ya faru a baya-bayan nan a Jenin - a yankin Yamma da Gabar kogin Jordan da ta mamaye - wanda Isra'ila ta sha kai hare-hare a wani bangare na yaƙi da 'yan ta'adda.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  20. An ga tankokin yaƙin Isra'ila a wajen asibitin yara

    Tun da farko, mun ba da rahoto game da halin da ake ciki a cikin ko kusa da asibitoci uku a arewacin Zirin Gaza da suka haɗa da asibitin Al-Shifa da Al-Quds, da kuma Asibitin Indonesiya.

    Yanzu haka an ba da rahoton gudanar wani aiki a wajen asibitin yara na Al-Rantisi a birnin Gaza.

    Shaidun gani da ido sun shaida wa BBC cewa sojojin Isra'ila na amfani da lasifika wajen umurtar ma'aikatan da ba majiyyata ba da su bar asibitin yaran.

    Isra'ila ta ce tana kai hari kan ramukan Hamas, ciki har da wasu asibitocin da ke karkashinta, a cewar rundunar tsaron Isra'ila.

    An kuma ba da rahoton cewa aƙalla mutum daya ya mutu a hari bama-bamai da aka kai a asibitin Al-Shifa na Gaza

    Hotunan da aka tabbatar sun nuna tankunan ƴakin suna aiki a wajen asibitin Al-Rantisi.

    ...