Qatar ta tabbatar da musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra'ila

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najieriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage and Haruna Kakangi

  1. Rufewa

    Nan za mu gintse kawo rahotonni a wannan shafi a yau Alhamis.

    Mu haɗu da ku gobe da safe don samun wasu sababbin rahotonnin.

    Mu kwana lafiya.

  2. Ɗaukar hoton mutane ya saɓa wa tsarin mulki - Ɗan majalisar Iran

    Dan majalisar Iran ya ce ɗaukar hoto ko bidiyon mutane ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar, tare da yinkira ga hukumomi da su fayyace dokar.

    Moinuddin Saeedi na mayar da martani ne kan masu ɗaukar bidiyo ko hotunan mutanen da ke sanye da hijabi.

    Dan majalisar - wanda ke wakiltar yankin Chabahar ya ƙara da cewa ba a bayyana masu kula da dokar sanya hijabin ga jama'a ba.

    "Don haka dole a fayyace waɗanda za su gudanar da aikin, samar da su aka yi, ko kuwa jami'an tsaro ne?, inda ba fayyace ba, to kenan aikin ba shi da inganci.

    Labarai da hotunan dakarun da ke kula da masu sanya hijabi, sun yaɗu a shafukan sada zumunta, inda mutane ke ta muhawara a kansu a faɗin ƙasar.

  3. Yarjejeniyar za ta ba da damar ƙara dakatar da faɗa ga duk mutum 10 da Hamas ta sako, Daga Frank Gardner, wakilin BBC kan harkokin tsaro

    Karin bayanin da Qatar wadda ita ce mai shiga tsakani, ta sanar a yau, a faɗaɗe ya ƙunshi wani tsari wanda wannan yarjejeniya ta sakin mutanen da aka yi garkuwa da su, za ta yi aiki.

    Daga karfe 6 na safe agogon Najeriya a gobe Juma'a, yarjejeniyar dakatar da faɗa ta tsawon kwana huɗu za ta fara aiki a Gaza.

    Daga ƙarfe 3 na rana agogon Najeriya, Hamas za ta saki rukunin farko na 'yan Isra'ila su 13 da ta yi garkuwa da su, inda za ta damƙa su a hannun ƙungiyar ba da agaji ta Red Cross.

    Da zarar sun fito ne, Isra'ila kuma za ta saki Falasɗinawa fursunoni 39 da take tsare da su a gidajen yarinta.

    Indai komai ya tafi daidai, za a ci gaba da maimaita haka, har fiye da tsawon kwana uku, ya zuwa lokacin da za a saki mutum 50 a cikin waɗanda ake gakuwa da su a Gaza, a madadin fursunoni Falasdinawa 150, da kuma gagarumin kari a kan kayan agaji da man fetur din da ake shigarwa Zirin Gaza.

    Isra'ila ta bayyana karara cewa za ta ci gaba da kai wa Hamas hari duk da haka, abin da dukkan kasashe a yankin suka nuna adawa da shi.

    Sai dai, yarjejeniyar ba ta bayar da damar karin kwana 1 na dakatar da fada ga duk wani karin rukunin mutum goma da Hamas ta saki.

  4. Sojojin Isra'ila sun tsare shugaban asibitin Al-shifa

    .

    Asalin hoton, Press Eye

    Sojojin Isra'ila sun tsare shugaban asibiti mafi girma a Gaza na Al-shifa.

    Wakiliyar BBC ta ce sojojin Isra'ila sun tabbatar da kama daraktan asibitin da wasu ma'aikatan lafiya goma.

    Tun farkon ɓarkewar rikicin, dakarun Isra'ila sun sha nanata zargin Hamas na amfani da babban asibitin na Gaza wajen kai hare-hare.

    Sojojin sun yi zargin cewa Hamas ta kai wasu daga cikin waɗanda ta yi garkuwa da su asibitin tare da kashe daya daga ciki a harabar asibitin, zargin da Hamsas ɗin ta musanta.

  5. Ma'aikatar lafiyar Hamas ta ce hari kan makarantar MDD ya kashe mutum 27

    Ma'aikatar lafiyar Hamas ta ce mutum 27 sun mutu bayan wani hari da ya faɗa kan wata makarantar Majalisar Dinkin Duniya a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza

    Sai dai BBC ta ba iya tabbatar da wannan iƙirari ba, amma za mu kawo muku ƙarin bayani da zarar mun samu.

    Ba wanna ne karon farko da aka kai hari kan makarantar ba, a ranar 2 ga watan Nuwamba ma wani hari ya faɗa makarantar.

    Inda Hukumar Agajin Falasɗinawa ta Majalisar Dinkin Duniya, UNRWA, ta ce mutum 20 ne suka mutu a lokacin harin.

  6. Turkiyya ta ƙara kuɗin ruwa da kashi biyar

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Babban bankin Turkiyya ya ƙara kuɗin ruwa da fiye da kashi biyar cikin dari, a yunƙurin da ƙasar ke yi na shawo kan hauhawar farashi.

    Matakin ya sanya kuɗin bashi ya koma kashi 40. Hakan na cikin jerin sauye-sauye na baya-bayan nan da gwamnatin ƙasar ta ɗauka domin ɗaga darajar kuɗin ƙasar, wato Lira.

    Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan ya yi fice kan tsattsauran ra'ayi dangane da tattalin arziki musamman kan rashin amincewarsa da ƙarin kuɗin ruwa.

    Sai dai ra'ayin nasa ya sauya bayan da aka sake zaɓensa a watan Mayu.

  7. Dalibai kada ku ji tsoron kawo mana rahoton masu cin zarafin lalata a jami'o'i - ICPC

    .

    Asalin hoton, ICPC

    Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ICPC ta bukaci daliban manyan makarantu kamar jami'o'i, kada su ji tsoron kai rahoton duk wani korafi na cin zarafin lalata ga hukumar.

    Hukumar ta yi wannan kira ne yayin wani taron wayar da kai na wuni daya a kan cin zarafin lalata a manyan makarantu, wanda aka yi a shalkwatar hukumar ranar Laraba.

    Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na sada zumunta, ta ambato sakataren ICPC, Mista Clifford Oparaodu yana nunar da cewa daya daga cikin manyan kalubalen da ke nakasa yaki da cin zarafin lalata a manyan makarantu shi ne rashin kai rahoto daga mutanen da aka ci wa zarafi.

    Ta alakanta rashin kai rahotannin a kan tsoron fuskantar tsangwama da kuma ci gaba da uzzura musu.

  8. Shugaban Mulkin sojin Nijar ya kai ziyara Burkina Faso

    .

    Asalin hoton, Niger presidency

    Shugaban Mulkin sojin Nijar Janar Abdurrahmane Tiani ya kai ziyara Burkina Faso, mai makwabtaka.

    .

    Asalin hoton, Niger presidency

    Tun da farko shugaban na Nijar ya ziyarci ƙasar Mali, inda ya gana da shugaban mulkin sojin ƙasar Kanal Assimi Goita, kafin ya wuce Burkina

    .

    Asalin hoton, Niger presidency

    Ziyarar ta kasance ta farko da shugaban ke yi a ƙasashen waje tun bayan kifar da gwmnatin shugaba Mohamed Bazoum cikin watan Yulin da ya gabata.

    .

    Asalin hoton, Niger presidency

    Bayanan hoto, Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Capt Ibrahim Traoré ne ya tarbi shugaban na Nijar.
  9. Lokacin da wani gungun mutane ya sa wawa a babban kantin Nike da ke Los Angeles

    Wani cincirindon mutane ya daka wawa a kantin sayar da tufafi na Nike da ke Los Angeles, inda suka sace kayan da ya kai darajar dala 12,000.

    Bidiyon da 'yan sandan Los Angeles suka fitar ya nuna wani gungun matasa na fizgar tufafi daga karfen rataya kaya, sannan suna cika jakunkuna da kayayyaki.

    'Yan sanda sun ce gungun, wanda ya kunshi mutum 17 'yan tsakanin shekara 15 zuwa 20, sun tsere daga kantin a cikin motoci daban-daban.

    Masu bincike na neman taimako daga jama'a don shaida gungun mutanen da ake zargi.

    Bayanan bidiyo, Gungun mutane sun sa wawa a kantin sayar da tufafi na Nike da ke Los Angeles
  10. Mutum 75 sun mutu a wani tashin hankali kusa da iyakar kudancin Sudan

    Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu, Nicholas Haysom, ya ce aƙalla mutum 75 ne suka mutu cikin makonni biyu sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin mazauna yankin Abyei da ke kan iyakar Sudan da Sudan ta Kudu.

    Ya yi kira ga gwamnati da ta gudanar da bincike kan lamarin don rage fargaba a zukatan jama'a, ya kuma yi kira ga shugabannin al'umomin da kada su yi amfani da rikici wajen warware kowace irin matsala.

    Rikicin na yankin Abyei ya ɓarke ne tsakanin ƙabilun Ngok da Twic kan mallakar dukiyoyi.

    A farkon wannan makon ne wani shugaban al'umma ya zargi sojojin Sudan ta Kudu da shirya hare-hare tare da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai, zargin da sojojin suka musanta.

    Ofisoshin jakadancin Norway da Birtaniya da Amurka sun fitar da sanarwa da a cikin suke kira ga gwamnatin Sudan ta Kudu ta janye dakarunta daga Abyei domin daƙile rikicin.

    Duka ƙasashen Sudan da Sudan ta Kudu na iƙirarin mallakar yankin mai ɗimbin arzikin man fetur, to amma sun amince da yarjejeniyar gwamnatin wucin-gadin yankin a 2011.

    Sai dai masu rajin kare haƙƙin bil-adama na zargin duka ɓangarorin biyu da saɓa yarjejeniyar.

    A halin yanzu yankin na Abyei na ƙarƙashin ikon dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

  11. Kotun ɗaukaka ƙara ta mayar wa Gwamna Sule na Nasarawa nasararsa

  12. Jadawalin wasannin cike gurbi na Euro 2024

  13. Maguire ya yafe wa ɗan majalisar Ghana da ya yi masa shaguɓe

  14. Gobe Juma'a kotun ɗaukaka ƙara za ta yi hukunci kan zaɓen gwamnan Kaduna

    .

    Kotun ɗaukaka ƙara ta sanya gobe Juma'a 24 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Kaduna.

    Tun da farko Ashiru Kudan da jam'iyyarsa ta PDP ne suka shigar da ƙara a kotun sauraron ƙorafin zaɓe, suna ƙalubantar nasarar Sanata Uba Sani da jam'iyyarsa ta APC.

    A ranar 28 ga watan Satumba ne kotun ta yanke hukuncin da kowane ɓangare ke iƙirarin cewa shi ne da nasara.

    Daga nan ne duka ɓangarorin suka garzaya kotun ɗaukaka ƙara, inda suka ƙalubalanci hukuncin da karamar kotun ta yanke.

    A baya-bayan nan kotun ɗaukaka ƙara na ci gaba da yanke hukunci kan ƙararrakin zaɓen gwamnoni a Najeriya, inda wasu daga cikin hukunce-hukuncen ke ci gaba da jan hankulan mutane a faɗin ƙasar.

    • Abin da ƙwararru ke cewa game da hukuncin zaɓen gwamnan Kaduna
    • Abin da kotun zaɓen Kaduna ta ce kan zaɓen gwamna
  15. Abin da muka sani kan yarjejeniyar sakin mutanen da ake garkuwa da su a Gaza

    Majid Al-Ansari

    Asalin hoton, REUTERS

    Bayanan hoto, Qatari foreign ministry spokesman Majid al-Ansari

    Cikin sauri ga bitar abin da muka fahimta game da yarjejeniyar sakin mutanen da ake garkuwa da su kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar harkoki wajen Qatar Majid al-Ansari ya ba da sanarwa:

    • Matakin dakatar da fada zai fara aiki daga karfe 7 na safe ranar Juma'a, duka a arewaci da kudancin Zirin Gaza
    • Za a saki mutum 13 da ake garkuwa da su da misalin karfe 4 na yamma
    • Duk wadanda za a saki mata ne da kananan yara
    • Za a damka su hannun kungiyar ba da agaji ta Red Cross, amma ba a bayar da cikakken bayani ba kan hanyar da za su don fita daga Gaza
    • Qatar ta ce tana tsammanin za a saki fursunoni Falasdinawa "sakamakon sakin mutanen da ake garkuwa da su", amma ba ta bayar da adadi ba
    • Isra'ila ta ba da tabbacin cewa ta karbi jerin sunayen wadanda za a fara saki, kuma tana tuntubar danginsu
    • Hamas ta ba da tabbacin cewar matakin dakatar da fada zai fara aiki da karfe 7 na safe, kuma ta ce za a bar tankokin dakon man fetur guda hudu da manyan motoci dauke da kayan agaji 200 su shiga Gaza kullum a tsawon kwana hudun.
    • Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Qatar Majed Al-Ansari ya ce ya yi imani cikakken bayani na wannan shirin yana da "gamsarwa da karfafa zuciya". Ya kara da cewa: "Ban sani ba ko ya kamata na ce akwai kwarin gwiwa, amma muna da matukar kyawun fata, kuma irin kudurin da muka gani daga kowanne bangare, ya sanya mu zama masu cike da burin alheri."
  16. Simon Lalong ya karbi shaidar zama sanata

    Simon Lalong

    Asalin hoton, SIMON LALONG/FACEBOOK

    Tsohon gwamnan Filato, Mista Simon Lalong ya karbi takardar shaidar cin zabe daga hukumar zabe ta kasa INEC a yau Alhamis.

    Matakin ya zo ne, bayan kotun daukaka kara a ranar Talata 7 ga watan Nuwamba, ta tabbatar da nasarar da ministan kwadagon na Najeriya ya samu a karamar kotu, inda ta yi watsi da karar da abokin takararsa Napoleon Bali ya daukaka.

    Simon Lalong

    Asalin hoton, SIMON LALONG/FACEBOOK

    Karamar kotun ta soke zaben Napoleon Bali bisa hujjar cewa jam'iyyarsa ta PDP ba ta da halastaccen shugabanci a lokacin da ta tsayar da shi takara.

    Simon Lalong

    Asalin hoton, SIMON LALONG/FACEBOOK

    Sai dai, babu masaniya karara ko hakan na nufin Simon Lalong, zai ajiye mukaminsa na ministan kwadago wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada shi, watanni bayan kammala zaben watan Fabrairu, don wakiltar jama'ar Filato ta Kudu a majalisar dattijan Najeriya.

  17. Za a saki rukunin farko na mutanen da ake garkuwa da su da karfe 4 na yamma - Qatar

    Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Qatar ya bayar da karin haske kan yarjejeniyar da aka cimma wadda za ta kai ga sakin mutanen da ake garkuwa da su, a madadin dakatar da fada tsawon kwana hudu.

    An karbi wani jerin sunayen fararen hula da za a saki daga Gaza, in ji shi, kuma rukunin farko na fararen hula, za a sake su ne da karfe 4 na yamma a gobe Juma'a.

    Ya ce sharadin da aka bi wajen tantance duk wanda za a saki "kacokam ya ta'allaka ne a kan jin kan dan'adam" - "fitar da mata da kananan yara daga hanyar cutarwa, ba tare da wani bata lokaci ba".

  18. Sakataren wajen Birtaniya: Na ga abin da ba zan taba mantawa ba a Isra'ila, Daga James Landale Wakilin Diflomasiyya na BBC, daga kudancin Isra'ila

    Duk lokacin da 'yan siyasa suka kai ziyara Isra'ila a baya, sun saba zuwa don nuna juyayinsu a Yad Vashem, wani wurin tunawa da kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa na Holocaust a birnin Kudus.

    A 'yan kwanakin nan suna ziyartar daya daga cikin yankunan kibbutzim a kusa da Gaza inda Mahas ta yi wa 'yan Isra'ila kisan gilla ranar 7 ga watan Oktoba. To da safiyar nan, David Cameron shi ma ya yi hakan, inda ya je kibbutz Be’eri, a ziyararsa ta farko da ya kai Isra'ila a matsayinsa na sakataren harkokin wajen Birtaniya.

    Cikin rakiyar Eli Cohen, takwaransa na Isra'ila, David Cameron ya yi tattaki ta wasu layuka masu luf-luf da bishiyoyi na garin manoma, inda aka yi wa kusan mutum 100 kisan gilla, 'yan kilomitoci kalilan daga Gaza.

    Ya taka ya hau kan baraguzan gidajen da aka kona, wadanda har yanzu ba su da dadin gani da kaurin toka. Kuma bayan nan sai ya ce ya ga abubuwan da ba zai taba mantawa ba.

    Cameron ya roki kowanne bangare da ke cikin yarjejeniyar dakatar da fadan, ya tabbatar da ganin lamarin ya faru, ya kara da cewa dakatar da fada bisa muradin jin kai, abu ne mai muhimmanci don ganin an kai kayan agaji cikin Gaza, da kuma samun fitowar mutanen da ake garkuwa da su.

    Bayanan bidiyo, Sakataren wajen Birtaniya David Cameron na ziyara a Isra'ila
  19. Yunwa ta kashe mutum 50 a Habasha

    Aƙalla mutum 50 ne suka mutu a yankin Tigray da kuma Amhara da ke arewacin Habasha saboda fari da ya jawo yunwa, kamar yadda jami'ai a yankin suka shaida wa BBC.

    A cewar ofishin kare afkuwar bala'o'i na yankin Tigray, ya ce mutane 46 suka mutu bayan barin gidajensu da suka yi sakamakon fari.

    Shugaban ofishin Gebrehiwot Gebregziabher, ya ce an samu mace-macen ne a garin Yechilla.

    A garin Wag Hemra na yankin Amhara, akalla mutum shida ne da dabbobi 4,000 suka mutu saboda ƙarancin abinci, a cewar wani jami'i.

    Amurka da MDD sun dakatar da kai kayan agaji zuwa Habasha tsawon watanni biyar, bayan zarge-zargen satar abinci da ake yi.

    Matsalar jin kai, da yaƙi, da kuma sauyin yanayi ya jefa miliyoyin mutane dogara da agajin da ake kai wa.

    Yayin da arewacin Habasha ke fuskantar tsananin fari, ana sa ran kudanci da kuma gabashin ƙasar za su fuskanci mamakon ruwan sama da ba a taɓa gani ba.

    A cewar MDD, sama da mutane 40 ne suka mutu a baya-bayan nan, sakamakon ambaliya da kuma zaftarewar laƙa, inda da yawa daga cikinsu suka fito daga yanin gabashin Somali.

  20. Labarai da dumi-dumi, Yarjejeniyar dakatar da faɗa a Gaza za ta fara aiki daga 10 na safiyar Juma'a - Qatar

    Qatar, wadda ke shiga tsakani a rikicin Hamas da Isra'ila, ta ba da sanarwa game da yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi a Gaza, wadda za ta fara aiki daga safiyar Juma'a.

    Za a saki rukunin farko na mutanen da ake garkuwa da su a yammacin Juma'ar.