Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin namu na kai-tsaye nan muka kawo karshen shafin na yau.

    Sai kuma gobe da ikon Mai duka, za mu sake dawowa don ci gaba da kawu muku sabbin labarai

    Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. Faransa ta ce 'yan daba sun saki fursunoni a Haiti

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Ofishin Jakadancin Faransa a Haiti ya ce ƙungiyoyin ƴan daba sun taimaka wa fursunoni wajen tserewa daga gidan yarin da ke baban birnin kasar.

    A jiya Asabar da daddare ne gidan yarin Port au Prince mai dauke da fursinoni kusan 4,000 ya fuskanci hari, lamarin da ya sa fursunoni masu yawa suka gudu, ciki har da wadanda suka kashe shugaban kasa.

    Ofishin jakadancin ya shawarci masu tafiye-tafiye da su kaurace wa babbanbirnin kasar a halin yanzu.

    Hukumar kula da gidajen yarin kasar ta yi kira ga yansanda da sojoji masu motoci da makami su je gidan kurkukun don taimakawa.

    Gungun yan daba masu aniyar hambarar da firaiminista Ariel Henry ne ke iko da kashi 80 ba babban birnin kasar haiti.

    A ranar Juma'a firaimnistan ya je Kenya don tattauna batun girke dakarun kasa da kasa don kawo karshen karya dokoki a Haiti

  3. 'Isra'ila ta ce ba za ta aike da wakilai zuwa tattaunawar tsagaita wuta a Masar ba'

    Wani jami'in Isra'ila ya ce ƙasar ba za ta aike da tawaga don tattaunawar tsagaita wuta a birnin Alkahira ba.

    Kafofin yada labaran Isra'ila sun kara da cewar jami'in wanda suka boye sunansa ya ce an dauki matakin ne saboda kungiyar Hamas ba ta bayar da cikakken jerin sunayen mutanen da ke raye a Gaza ba.

    Hamas ta ce za ta saki wasu fursunoni da zarar an cimma yarjeniyar, kasashen ketare na ci gaba da matsa lamba don kara shigar da kayan agaji ko an cimma yarjejeniya ko ba a yi nasara ba.

    Da safiyar wannan rana tawagar Hamas ta isa birnin Alkahira domin tattaunawa da masu shiga tsakani daga kasashen Masar da Amurka da kuma Qatar.

    A baya-bayan nan ana sa rai da yiwuwar cimma yarjejeniya mai dorewa kafin Ramadan

  4. City ta caskara United a wasan hamayyar Manchester

  5. 'An kashe gomman mayaka masu ikirarin jihadi na Somaliya'

    b

    Kafar yada labaran gwamnatin Somaliya ta ce dakarun gwamnati sun kashe akalla mayakan al-shabab 30 a kusa da Jamaame, da ke kudancin birnin Mogadishu

    Akalla mayakan kungiyar 10 aka kama a wani abu da gwamnati ta kira da samamen hadin gwiwa a kauyukan da ke kewayen gauruwan da ke kusa da kogin Jubba.

    An ruwaito cewa dakarun gwamnati na yankin Jubaland ke suka kaddamar da smamen.

    A baya-bayan nan gwamnati ta tsananta kai samame kan maykan kungiyar al-Shabab a kudancin Somaliya inda mayaka masu alaka da kungiyar al-Qaeda ke iko da yankunan karkara.

  6. Suarez ya ci kwallonsa na farko a Miami

  7. Najeriya da Qatar sun cimma yarjejeniyoyin hadin gwiwa

    ..

    Asalin hoton, Ajuri Ngelale

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu da sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, sun sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi da za su bude kofar inganta muhimman fannoni tsakanin kasashen biyu.

    Bangaren da yarjejeniyoyin za su shafa sun hadar da fannonin ilimi da kasuwanci da inganta zuba jari, da sama wa matasa ayyuka da harkar ma'adinai da yawan bude ido da wasanni.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya ce an cimma yarjejeniyar ce a fadar sarkin Qatar.

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce a shirye kasarsa take don yin maraba da masu zuba jari, yana mai cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi na inganta zuba jari a kasar.

    Ya ce babban karfinmu shi ne mutanenmu. karfinmu ya dogara kan matasanmu. suna da karfi , da fikira da yarda da kansu," in ji shugaban na Najeriya.

    Ya kara da cewa matasan kasar na da ilimi kuma suna da fikirar neman sana'a a duk inda take.

    Shugaba Tinubu ya nada ministan kudi da na tattalin arziki, mista Wale Edun a matsayin wanda zai jagoranci tawagar gwamnatin Najeriya da za ta tattauna da hukumomin Qatar wajen gano bangarorin da za a zuba jarin da aiwatar da shi, don ciyar da kasar gaba.

    Shugaba Tinubu dai na ziyarar aiki a kasar Qatar tare da wasu manyan jami'an gwamnatinsa.

  8. An kori Bellingham a wasan da Real ta yi canjaras da Valencia

  9. Mutanen da suka ceci ran juna duk da ba su taɓa haɗuwa ba

  10. An hallaka mutum 170 a wani hari a Burkina Faso

    Burkina Faso attacks

    Asalin hoton, AFP

    Kimanin mutum 170 da suka haɗa da mata da ƙananan yara ne aka kashe a harin da aka kai wasu kauyuka uku a Burkina Faso, a cewar wani mai gabatar da ƙara.

    Aly Benjamin Coulibaly ya roki shaidun gani da ido da su taimaka wajen nemo waɗanda suka kai hari kauyukan Komsilga, Nordin da kuma Soro.

    A nasu ɓangaren, hafsoshin sojin ƙasar sun yi gargaɗin cewa za a samu ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga, ciki har da hare-haren kan birane.

    Sojojin ƙasar sun kwace mulki a Burkina Faso a shekarar 2022, amma masu ta da ƙayar-baya ne ke iko da sama da kashi uku na ƙasar.

    Mista Coulibaly ya ce ya kaddamar da bincike kan hare-haren da aka kai kauyukan da ke lardin Yatenga a ranar 25 ga watan Fabrairu.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa gomman mata da ƙananan yara ne suka mutu a harin.

    Zuwa yanzu dai, ba a san wace ƙungiya ce ta kai hare-haren ba.

  11. An karrama ɗan agajin da ya tsinci fiye da naira miliyan 100 ya mayar

    Gwamnan Bauchi da ɗan agaji

    Asalin hoton, Jibwis Bauchi State

    Ƙungiyar Izala ta ƙasa, JIBWIS ta karrama wani matashin ɗan agaji da ya tsinci kuɗi sama da naira miliyan 100, sannan ya mayar da su.

    Cikin wani sako da ƙungiyar reshen jihar Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce matashin ɗan agajin mai suna Salihu AbdulHadi Kankia, ya taka rawar gani, wanda ya kai a jinjina masa.

    A wurin rufe taron ƙara wa juna sani na malamai masu gabatar da tafsiri, Daraktan Agaji na ƙasa Injiniya Mustapha Imam Sitti ya gabatar da matashin wanda ya tsinci jaka cike da makudan kuɗi da suka kai sama da naira miliyan 100 a Kankia da ke jihar Katsina.

    ''Salihu ya ɓoye kuɗin a gida, sannan ya garzaya zuwa ofishin ƴansanda ya sanar musu cewa ya tsinci jaka a yi cigiya wa al'umma amma jakar tana wurinsa'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Kan wannan abin a yaba ne ƙungiyar ta Izala ta karrama matashin da lambar yabo tare da ba shi kyautar kujerar Hajjin bana.

    ''Sannan kuma Hon. Abdulmalik Zannan Bangudu (Ɗan Agaji kuma Dan Majalisa a Jihar Zamfara) ya bashi kyautar miliyan biyu'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Ɗan Agaji

    Asalin hoton, Jibwis Bauchi State

    Bayanan hoto, Salihu AbdulHadi Kankia

    Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed ya ba shi kyautar mota kirar bas don ya kama sana'a..

    Tsintar makudan kuɗi a kuma mayar da su musamman a wannan yanayi da ake ciki na matsin rayuwa, abin a yaba ne.

    Ko a shekarar da ta gabata ma wani matashi mai tuka keke Napep a Kano ya tsinci kuɗi kimanin naira miliyan 14 tare da mayar da su ga mai su.

    Lamarin da ya sa matashin ya samu kyaututtuka masu ɗimbin yawa a ciki da wajen jihar.

    Haka ma a shekarar da ta gabata, gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya karrama wata mata da ta tsinci wasu makudan kuɗaɗe sannan ta mayar da su a lokacin aikin hajjin da ya gabata.

    Ɗan Agaji

    Asalin hoton, Jibwis Bauchi State

  12. Ya ya tsarin gwamnati na barin kasuwa ta yi halinta a kan kuɗaɗen waje yake?

    Shirin Amsoshin Takardunku na wannan mako ya yi duba kan batun tsarin gwamnatin Najeriya na baya-bayan na cewa kasuwa ta yi halinta a kan kuɗaɗen waje musamman ma dala.

    Har ila yau shirin ya kuma amsa tambaya kan yadda ya kamata mutum ya yi tsutsar kunne.

    Muhammad Annur Muhammad ne ya gabatar da shirin.

    Bayanan sautiLatsa sama don sauraron shirin
  13. Fusatattun mutane sun fasa rumbun abinci tare da yin wawaso a Abuja

    Wawaso

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu fusatattaun matasa sun fasa rumbun adana abinci na gwamnati da ke unguwar Gwagwa a Abuja, babban birnin Najeriya, tare da yin wawason kayan abinci.

    Matasan sun yi wa rumbun dirar mikiya ne da misalin karfe 7 na safe, inda suka yi wawushe buhunan masara da kuma na hatsi.

    Mai magana da yawun ƴansandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatarwa da BBC faruwar lamarin, inda ta ce tuni suka tura jami'ansu zuwa yankin domin shawo kan lamarin.

    Rahotanni sun bayyana cewa fasa rumbun abincin ya janyo cushewar hanyar Gwagwa-Karmo, wadda kuma ta dangana da anguwan Dei-Dei da kuma wani ɓangare na Jabi.

    Ƴan Najeriya da dama dai na ci gaba da kokawa kan matsin rayuwa da suke ciki biyo bayan janye tallafin man fetur da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi.

    Tsare-tsaren tattalin arziki da gwamnatin ta zo da su, sun janyo hauhawar farashin kayan abinci wanda ba a taɓa gani ba a baya-bayan nan.

  14. Amurka ta kai kayan agaji karon farko ta sama zuwa Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta kai agaji na farko a zirin Gaza, inda jirage guda uku suka harba wa mutane sama 30,000 abinci daga sama.

    Wannan shi ne karon farko da Amurka ta kai agaji zuwa Gaza tare da haɗin gwiwar sojojin saman ƙasar Jordan, bayan sanarwar da shugaba Joe Biden ya yi na cewa za su kai agaji.

    Shugaban wata fitacciyar ƙungiyar agaji ya shaida wa BBC cewa akwai tsananin yunwa a arewacin Gaza.

    Akalla mutum 112 ne suka mutu yayin da jama’a lokacin da jama'a suka yi ribibin karɓar kayan agaji a wajen birnin Gaza ranar Alhamis.

    Hamas dai na zargin waɗanda suka kawo agajin da kisan mutanen. Isra'ila ta musanta hakan kuma ta ce tana gudanar da bincike.

    Jirgin na farko na Amurka ya zo ne a daidai lokacin da wani babban jami'in Amurka ya ce tsarin yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako shida a Gaza na ƙasa.

  15. Rundunar ‘yansanda a Katsina ta sanya ladan miliyan 50 kan wasu ‘shugabannin ‘yan fashi’

    Ƴansanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ‘yansanda a jihar Katsina ta sanya ladan miliyan 50 kan wasu ‘shugabannin ‘yan fashi’ guda biyu.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar Asp Abubakar Sadiq ya fitar, ta ce duk wani wanda zai taimaka da bayanai da za su kai kamo shugabannin ƴan fashin masu suna 'Modi Modi' da kuma 'Jan Kare' zai samu ladar miliyan 50.

    Asp Abubakar ya ce ƴan fashin sun kasance suna cin karensu babu babbaka a jihar ta Katsina, musamman ma yankuna da ke ƙananan hukumomin Kankara da kuma Safana.

    "Samar da tsaro na da muhimmancin gaske, shi ya sa gwamnatin jihar Katsina da ƴansandan jihar da kuma sauran hukumomin tsaro suka ɗauki aniyar magance duk wasu masu tayar da zaune tsaye da hana zaman lafiya a faɗin jihar," in ji Asp Abubakar.

    Ya ƙara da cewa sun yi tayin bayar da ladan kuɗin ne a ƙoƙarinsu na ganin an yi wa mutane adalci, ganin cewa batun tsaro hakki ne da ya rataya wuyan kowa.

    Ya kuma ce hakan zai sa a kawo karshen ayyukan ɓata-gari a jihar.

    Kakakin ƴansandan ya ce rundunar na kira ga kowane ɗan jihar da ya zo ya gabatar da bayanai da za su taimakawa jami'an tsaro wajen kama waɗanda ke sahun gaba a yin garkuwa da mutane da kuma fashi.

  16. 'Magance matsalar tsaro nauyi ne da ke wuyan kowane ɗan ƙasa'

    Yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da zama wani karfen kafa a Najeriya, wasu tsofaffin ɗaliban cibiyar koyar da tsare-tsare da dabarun mulki ta ƙasar, wato NIPSS, suna ganin fafutukar magance matsalar tsaro wani nauyi ne da ke wuyan kowane ɗan ƙasar.

    Sun kuma bayar da shawarwari na hanyoyin da ya kamata a bi don tabbatar da hakan.

    A hirarsa da Abdussalam Ibrahim Ahmed, Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka mai ritaya, ɗaya daga cikin tsofaffin ɗaliban cibiyar, ya ce sun bayar da shawarwarin ne a wajen wani taro da sukan gudanar a duk shekara a babban birnin tarayya Abuja.

    Bayanan sautiLatsa sama don sauraron tattaunawar
  17. Sojojin ruwan Najeriya sun kama jirgin ruwa da ake zargi da satar ɗanyen mai

    Jirgin ruwa

    Asalin hoton, Nigerian Nav/X

    Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ta Kama wani jirgin ruwa na ƙasar Ghana wanda ake zargin yana da hannu wajen satar ɗanyen man fetur.

    Rundunar sojin ruwan ta ce ta kama jirgin ruwan ne mai rijista da ƙasar Ghana, wanda kuma ake zarginsa da satar mai.

    An kama jirgin kusan mil 174 daga gaɓar ruwan Najeriya, mai kuma tazarar kilomita 320 lokacin da ya nufi Jamhuriyar Benin.

    Jami’in yaɗa labarai na rundunar sojin ruwan Najeriya, Laftanar Hussaini Ibrahim, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa jirgin na ɗauke da ma’aikata 13 a lokacin da aka kama shi, ‘yan Najeriya 12 da kuma ɗan Ghana ɗaya.

    Sanarwar ta ce na ɗauke da kusan lita miliyan biyu na ɗanyen mai.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Cutar Kyanda ta ɓarke a Kano

    Kyanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a karamar hukumar kwaryar birnin Kano da ke jihar Kano sun tabbatar da ɓarkewar cutar kyanda a wasu sassan karamar hukumar.

    Shugaban kula da lafiya matakin farko na yankin, Aliyu Jinjiri Kiru ne ya bayyana hakan a lokacin wani taro na kwamitin bayar da agajin gaggawa a sakatariyar karamar hukumar.

    A cikin wata sanarwa da jami’ar yaɗa labaran yankin, Fatima Abdullahi ta fitar, ta ruwaito shugaban na cewa sun samu rahoton ɓarkewar kyanda da sauran cututtuka masu yaɗuwa daga cibiyoyin kiwon lafiya da dama a karamar hukumar.

    Aliyu ya ce yankunan da ake zargin ɓullar cutar sun haɗa da Sharada, Madatai, da Gandun Albasa.

    Ya yi kira da a ɗauki matakin gaggawa don shawo kan cututtukan.

    A nasa ɓangaren, jami’in kula da harkokin yaki da cututtuka Tukur Hassan, ya ce tuni suka mika waɗanda ake zargi sun kamu da cutar zuwa asibitin Murtala domin killace su.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hakimin karamar hukumar, Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani, ya yi kira ga dukkan masu unguwanni da su ba da fifiko kan harkokin kiwon lafiyar jama’a a kowani lokaci saboda muhimmancinsa.

  19. Senegal: Masu zanga-zanga sun buƙaci a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa nan take

    Senegal

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗaruruwan masu zanga-zanga ne suka cika titunan Dakar, babban birnin Senegal, tare da kiran a gudanar da zaɓe kafin wa'adin mulkin shugaba Macky Sall ya kare a watan Afirilu.

    Mr Sall ya fusata 'yan ƙasar bayan ɗage babban zaɓen da aka shirya yi a watan da ya wuce, da kuma kasa bayyana lokacin da za a yi.

    A ranar Asabar, masu zanga-zangar da suka haɗa da jam'iyyun siyasa da masu rajin kare hakkin ɗan adam, suka kira Mr Sall da mai mulkin danniya.

    Sun kuma buƙaci a sako jagoran adawa Ousmane Sonko daga gidan yari.

    A makon da ya wuce jam'iyyun adawa sun kauracewa zaman tattaunawa da wakilan da ke shiga tsakani domin warware rikicin siyasar Senegal waɗanda shugaba Sall ne ya samar da su, sun kuma ba da shawarar gudanar da zaɓen a watan Yuni mai zuwa.

  20. Yaƙin Gaza: Za a ci gaba da tattauna buƙatar tsagaita wuta a Masar

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Nan gaba a yau ake sa ran masu shiga tsakani za su isa birnin Alkhahira na Masar domin tattauna yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi tsakanin Isra'ila da Hamas.

    Majiyar jami'an tsaron Masar ta ce ana sa ran wakilan Isra'ila da Hamas za su halarci zaman na yau.

    Wani babban jami'in Amurka ya ce Isra'ila ta amince da sake duba batun tsagaita wuta ta makonni shida a Gaza.

    Jami'in ya ce tsagaita wutar ka iya fara aiki nan take idan Hamas ta amince ta saki masu rauni cikin Isra'ilawan da ta yi garkuwa da su.