Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Ahmad Tijjani Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Mutum ɗaya ya mutu sannan wasu goma kuma suka jikkata bayan da wata mota da ke tafiya saman igiya wato 'Cable car' ta yi karo da wata sanda da ta karye a kudancin ƙasar Turkiyya.
Fasinjoji sun kife kasa bayan afkuwar hatsarin a yammacin ranar Juma'a bayan da wani abu da ke taimaka a motar ya lalace a kusa da birnin Antalya.
Ɗaukacin motar ta lalace yayin da ma'aikatan gaggawa suka yi ƙoƙarin kwashe fasinjojin da suka makale.
Ma'aikatar shari'ar ƙasar ta ce an buɗe bincike kan hadarin.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Turkiyya ta ce an ceto fasinjoji 128 daga cikin motocin guda 16 a daren Juma'a a gundumar Konyaaltı da ke Antalya.
Amma jami'ai sun ce fasinjoji 43 na ci gaba da maƙale har zuwa safiyar Asabar ɗin nan.
Jiragen sama masu saukar ungulu bakwai da masu aikin ceto sama da 500 da suka haɗa da kwararrun masu hawan tsaunuka sun kasance a wurin a ranar Asabar, kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gidan Turkiyya ta wallafa a shafinta na sada zumunta.

Asalin hoton, Getty Images
An zargi Iran da kawace wani jirgin ruwa mai alaƙa da Isra'ila da sanyin safiyar Asabar a lokacin da yake wucewa ta mashigin Hormuz.
Dakaru na musamman na Iran ne suka hau jirgin na MSC Aries mai nisan kilomita 80 daga gaɓar tekun Haɗadɗiyar Daular Larabawa, a cewar sanarwar da MSC ta fitar.
Hotunan da kamfanin dillancin labarai na AP ya samu sun nuna yadda sojoji ke sauka cikin jirgin da igiya daga wani jirgi mai saukar ungulu.
Wannan jirgi mai ɗauke da tutar ƙasar Portugal yana da alaƙa da hamshaƙin attajirin nan na Isra'ila Eyal Ofer.
Lamarin dai ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa game da harin da Iran ta kai kan Isra'ila bayan wani hari ta sama ya lalata ofishin jakadancin Iran da ke Damascus a farkon watan Afrilu.

Asalin hoton, Daddy D.O/X
Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a samar da haɗin kai tsakanin gwamnatin tarayya, gwamnonin jihohi da kuma ƴan majalisar tarayya don kawowa Najeriya ci gaba.
Shugaban ya yi wannan kira ne lokacin da ya karɓi bakuncin gwamnonin jihohi da kuma shugabancin majalisar tarayya a gidansa da ke Legas ranar Juma'a.
Tawagar wadda ta samu jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ta kunshi shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas, gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya da sauransu.
Da yake magana a madadin shugaban ƙasar, Shettima ya yi fata kan farfaɗowar tattalin arzikin Najeriya, inda ya yi kira ga haɗin kan kowa domin kai ƙasar gaba.
Ya buƙaci haɗin tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki tare da yin alkawarin makoma mai kyau ga ƙasar karkashin jagorancin shugaba Tinubu.

Asalin hoton, Daddy D.O/X

Asalin hoton, Daddy D.O/X
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Sabuwar majalisar dokokin Ecowas zango na shida da aka ƙaddamar a baya-bayan nan, ta ce za mayar da hankali wajen ganin ta inganta haɗin kai da ƙarfafa zumunci tsakanin ƙasashen yankin Afirka ta Yamma.
A ranar 6 ga watan Afrilun nan ne, aka ƙaddamar da sabuwar majalisar a Abuja, babban birnin Nijeriya, daidai lokacin da Ecowas ke fuskantar babban ƙalubale na barazanar ɓallewar wasu ƙasashe mambobinta.
Sabon shugabancin majalisar dokokin na Ecowas, ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ƙasashen, sun koma kan turbar dimokraɗiyya.
Kan haka Buhari Muhammad Fagge ya tattauna da Sanata Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattijai ta Najeriya, kuma mataimakin shugaban majalisar Ecowas na ɗaya, kuma mai riƙon muƙamin kakaki, ya zuwa lokacin da za a zaɓi tabbataccen shugaba daga ƙasar Togo.
BBC ta yi Alla-wadai da matakin Rasha na ayyana ɗaya daga cikin ma'aikatanta, Ilya Barabanov, a matsayin ɗan leƙen asiri.
Wannan batu dai zai yi mummunan tasiri, da dakushe muryoyin ba masu sukar matakin Rasha na mamayar Ukraine kaɗai ba, har da masu sukar manufofin Kremlin.
BBC dai ta jaddada cewa itakafar yaɗa labarai ce mai mutunci da tsage gaskiya, kuma hanyar da Rashawa suka dogara da ita wajen samun sahihan labarai sama da shekaru 80.
Mista Barabanov da wani ɗan jarida, Asya Kazantseva ne dai aka ayyana da masu leƙen asirin, waɗanda dukkanninsu na zaune a ƙasashen waje.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ‘yan sandan birnin Sydney ta ce adadin mutanen da suka mutu a harin wuka da aka kai a kasuwar Sydney ya yi sanadin mutuwar mutane shida tare da jikkata wasu takwas ciki har da wani karamin yaro wanda ake yi masa tiyata a yanzu.
Biyar daga cikin mutane shida da suka mutu mata ne.
‘Yan sanda sun ce suna binciken domin gano maharin.
A wani taron manema labarai da ɗaya daga cikin shugabannin rundunar ‘yan sandan Webb ta yi, ta shaida wa manema labarai cewa za a gudanar da bincike sosai, kuma za a ɗauki kwanaki kafin a kammala.
Da take mayar da martani ga manema labarai da suka tambayi dalilin da ya sa ‘yan sandan ke da yakinin cewa harin ba shi da alaƙa da ta’addanci, ta ce: “Akwai abubuwan da muka fahimta a halin yanzu da ba su nuna hakan ba, amma yayin da muke gudanar da bincike, da kuma tarihin wannan mutumin - sai mun gano gidansa, motarsa, abokansa, sannan komai zai fito fili."
Wani ɗan sanda dai, ya harbe maharin mai shekaru 40 nan take a wurin da lamarin ya faru.

Asalin hoton, Nigerian Army/X
A ranar Juma'a n,Owowoh Princess Oluchukwu, ta zama mace ta farko ƴar Najeriya da ta kammala karatu a Kwalejin sojoji ta Sandhurst da ke Birtaniya.
Oluchukwu mai shekaru 24, ta kasance ɗaya daga cikin jami'an Cadets 135 da suka kammala karatu yayin wani fareti da aka shirya a birnin Landan a ranar ta Juma'a.
A shekarar 2018, Princess ta shiga makarantar horas da sojoji ta Najeriya (NDA), a jihar Kaduna.

Asalin hoton, Nigerian Army/X
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, FCT Police Command/X
Rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja, ta ce ta kama mutum da shida waɗanda take zargi da sata da kuma lalata transfoma na bayar da hasken wutar lantarki.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan, SP Josephine Adeh ta fitar, ta ce ta kama mutanen ne a ranar Alhamis 11 ga watan Afrilun, 024 a Tipper Garage da ke anguwar Mpape.
Adeh ta ce an kama su ne lokacin da suke ƙoƙarin tserewa da wata transfoma wadda suka saka cikin wata motar ɗaukar kaya a Maitama, kuma cikinsu har da wani ma'aikacin kamfanin rarraba hasken lantarki na babban birnin tarayya.
Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan mutanen,vkwamishinan ‘yan sanda na Abuja, CP Benneth C. Igweh, ya sake jaddada aniyarsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a al'umm a birnin.
Ya kuma buƙaci mazauna yankin da su yi taka tsan-tsan tare da yin amfani da layukan gaggawa na ‘yan sanda wajen bayar da rahoton abubuwan da ba su yarda da su ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Reuters
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, zai yi balaguro zuwa China a ziyarar da ake ganin Beijing za ta matsa masa kar ya mara baya ga matakin Tarayyar Turai na takaita motoci masu amfani da lantarki da sauran kayan fasaha da ta ke fitarwa.
Ana kuma sa ran shugaba Sholfz zai gana da takwaransa na China Xi Jinping a ranar Talata inda za su tattauna kan yakin Gabas Ta Tsakiya da na Ukraine.
China babbar aminiyar Jamus ce ta fuskar kasuwanci, kuma tattalin arzikin kasashen biyu na bunkasa.
Olaf Scholz zai kuma tafi China da tawagar wakilan manyan kamfanonin kasar ciki har da Siemens da Mercedes.
Dandazon mutane ne suka fito a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar tare da buƙatar sojojin Amurka da na sauran ƙasashe su fice daga ƙasar.
Nijar dai tuni taa soke yarjejeniyar soji da Amurka a watan ya gabata, kuma hakan na zuwa ne 'yan watanni bayan da hukumomin sojin ƙasar suka yanke irin wannan alaƙa da Faransa, inda har ma aka kori dakarun tsohuwar uwar gijiyar tata ta mulkin mallaka da ke yakar masu ikirarin jihadi a yankin daga ƙasar.
Yanzu dai ƙasar tana kusanta kanta ga Rasha domin samun tallafi wajen yaƙar masu iƙirarin jihadi.
Kuma a ranar Laraba ne ƙwararrun sojoji daga Rasha suka isa domin horas da sojojin ƙasar.







Asalin hoton, Getty Images
Kamfanonin jirage da dama sun ɗauki matakin kauracewa sararin samaniyar Iran, a daidai lokacin da rikici ke kara kamari a yankin.
Jirgin Qantas na Australia da Lufthansa na Jamus na karkata akalarsu ta bin hanyoyi masu nisa, yayin da aka dakatar da dukkan jirage daga ƙasashen yamma zuwa Iran inda suka bi sauran takwarorinsu da suka kaucewa bin ƙasar.
A ranar Juma'a shugaba Joe Biden na Amurka, ya ce ya yi amanna babu abin da zai hana Iran mayar wa Isra'ila kakkausan martani, amma duk da hakan ya yi kakkausan gargaɗi ga ƙasar kada ta kuskura ta aikata hakan.
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Amurka sun girke kayan aiki a Isra'ila domin ba ta kariya.

Asalin hoton, Anadolu/Getty Images
Isra'ila ta ce sojojinta sun kaddamar da hari na tsakar dare kan Hamas a tsakiyar Gaza, inda suke nausawa yankunan da ke wajen sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat wanda ayyukan sojin bai lalata sosai a baya ba.
Sojojin sun yi ruwan hare-hare ta sama kafin daga bisani wasu suka danna yankin ta kasa, kuma mutum biyar ne suka mutu a harin.
A ɓangare guda kuma, an kashe wani Bafalasɗine,da jikkata wasu 25 bayan yahudawa 'yan kama wuri zauna sun afkawa kauyen al-Mughayyir da ke kusa da birnin Ramallah a Gaɓar Yamma.
Lamarin ya faru bayan sojin Isra'ila da dakaru na musamman sun zo neman wani yaro ɗan shekara 14 da ya ɓata.
Benjamin Achimeir ya fito kiwon dabbobi daga wani matsugunin 'yan kama wuri zauna da ke kusa da kauyen, tun daga lokacin ba a kara ganinsa ba.
Masu bibiyar mu barkan mu da warhaka.
Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.
Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran sassan duniya.
Ahmad Tijjani Bawage ne zai kasance da ku tsawon yinin yau.