Bankwana
A nan muka kawo ƙarshen rahotannin shafin kai tsaye na BBC Hausa a yau Lahadi.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Ahmad Bawage da Badamasi Abdulkadir Mukhtar
A nan muka kawo ƙarshen rahotannin shafin kai tsaye na BBC Hausa a yau Lahadi.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Likitoci sun ce mutane fiye da 60 sun samu rauni a wani harin jirgin sama marar matuƙi da aka kai yankin Binyamina a arewacin Isra'ila.
Sanarwar da ƙungiyar likitoci masu aikin ceto ta United Hatzalah ta fitar ta ce daga cikin mutanen akwai masu tsananin rauni, kuma akwai waɗanda raunin nasu bai yi ƙamari sosai ba.
Ta kuma bayyana cewa dukkanin su suna asibiti inda ake kula da su.
Hezbollah ta ce ita ce ta kai harin, wanda a cewar ta tayi niyyar ya faɗa ne a kan sansanin horas da dakarun Isra'ila a tsakanin Tel Aviv da Haifa.
Ƙungiyar ta ce harin martani ne kan hare-haren da Isra'ila ta kai kudancin Lebanon da kuma Beirut a ranar Alhamis.

Asalin hoton, EPA
Isra'la ta ce tankokin yaƙin ta sun yi taho mu gama da jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kudancin Lebanon, bayan jami'an sun zargi sojojin Isra'ilar da lalata babbar kofar shiga wurinsu da jefa musu hayaƙi mai sa hawaye.
Sai dai sanarwar da sojin Isra'ilar suka fitar, ta ce abokan gaba ne suka kawo mu su hari, a lokacin da suke ƙoƙarin ɗauke sojojinsu da suka jikkata kuma sun yi nisa da sansaninsu.
Majalisr Dinkin Duniya dai ta yi allawadai da harin da aka kai wa jami'an nata, kuma ta je dakarun Isra'ilan sun kutsa kai da ƙarfi ne a cikin ofishin jami'an nata a ranar Lahadi.
Ana ci gaba da gwabza yaƙi ta ƙasa a tsakanin ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon da kuma Isra'ila.
An kuma tabbatar da cewa harin jirgi maras matuƙi ya hallaka gomman mutane arewacin Lebanon.
Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Unifil ta ce dakarun Isra'ila sun ɓalle babbar ƙofar shiga ofishin ta da ke Ramyah, tare da neman a kashe wutar lantarki a ofishin.

Asalin hoton, @SERAPNIGERIA
Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya, ta buƙaci a gaggauta janye ƙarin farashin man fetir a ƙasar.
Ƙungiyar ta buƙaci shugaba Bola Tinubu ''ya umarci kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya gaggauta soke ƙarin farashin man da yayi, wanda shi ne karo na biyu a cikin wata ɗaya, har zuwa lokacin da za a samu hukuncin kotu a kan ƙarar da aka shigar domin ƙalubalantar ƙarfin ikon kamfanin NNPCL game da ƙara farashin mai a ƙasar.''
A watan da ya gabata, ƙungiyar SERAP ta shigar da ƙara, inda take neman kotu ta tilastawa shugaba Tinubu da kamfanin NNPCL ''mayar da farashin man fetir a yadda ya ke kafin ƙarin, da kuma neman a gudanar da bincike a kan almundahanar da ake zargin ana tafkawa a kamfanin NNPCL.''
Mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya ce “Sabon ƙarin farashin man fetir ɗin a daidai lokacin da ake gaban kotu domin tantance ƙarfin ikon masu alhakin ƙara farashin, cin fuska ne ga tafarkin shari'a''
SERAP ta buƙaci shugaba Tinubu ya gaggauta bayar da umarnin dakatar da sabon farashin man har zuwa lokacin da kotu ta yanke hukunci a game da ruɗanin da aka shiga na neman tantanci wanda ke da ƙarfin ikon ƙara farashin mai a Najeriya.

Asalin hoton, Reuters
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce ƙasarsa ''a shirye take ta shiga yaƙi''
Da yake jawabi a yayin wata ziyara a Baghdad, Abbas Araghchi ya ce ''Mun shirya tsaf domin fuskantar duk wni yanbayin yaƙi. Ba mu tsoron yaƙi ama kuma ba mu son yaƙi, mun fi ƙaunar zaman lafiya''
Ya kuma bayyana cewa Iran ''za ta yi aiki domin wanzar da zaman lafiya a Gaza da kuma Lebanon.''
Ministan hrkokin wajen Iran ɗin ya ziyarci Iraqi ne domin tattauna hanyoyin kawo ƙarshen yaƙi a Lebanon da Gaza.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Biden ya isa Florida kuma daga nan zai ƙarasa wasu yankuna da mummunar guguwar Milton ta shafa a ranar Laraba.
Guguwar mai ƙarfin gaske ta zo da ruwan sama a wasu sassan, kuma mutane aƙalla 23 ne aka tabbatar ta kashe.
A yayin ziyarar, Mista Biden zai gana da wasu daga cikin mutanen da guguwar ta shafa, da kuma waɗanda ke taimakwa wajen kwashe gyaran da ta yi.
Ana sa ran ziyarar ta ɗauki salon siyasa inda shugaba Biden zai yi amfani da damar da ya samu wajen neman majalisa ta amince d ƙarin kuɗin tallafi, gabanin zaɓen ranar biyar ga watan Nuwamba.
Majalisar dokokin Amurkan ba za ta dawo daga hutu b har sai bayan zaɓen kuma ana bayyana damuwa game da tallafin kuɗin wasu ayyukan da suka kusa ƙarewa, waɗanda ake bukatar zuba masu ƙarin kuɗaɗe cikin gaggawa.
Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a wasu yankuna da ke kudancin Lebanon.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Fafaroma Francis ya yi kira da a 'mutunta' jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke aiki a Lebanon.
Fafaroma ya bayyana haka ne bayan jikkata wasu jami'an MDD biyar a kudancin Lebanon.
"Ina kusa da dukkan mutanen da wannan abin ya shafa kama daga Falasɗinawa da Isra'ilawa da kume ƴan Lebanon, inda na buƙaci a mutunta jami'an wanzar da zaman lafiya," in ji Fafaroma yayin da yake magana a fadarsa ta Vatican.
"Ina ƙara yin kira da a tsagaita wuta nan take tsakanin ɓangarori, sannan a bi matakin tattaunawa da kuma diflomasiyya domin samun zaman lafiya," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu ‘yan bindiga sun buɗe wa wani fitaccen ɗan siyasa a Mumbai babban birnin kasuwancin Indiya wuta.
An harbi Baba Siddique mai shekaru 66 ne a kusa da ofishin ɗansa, wanda shi ma ɗan siyasa ne.
Baba Siddique jigo ne a siyasar jihar Maharashtra inda ake sa ran gudanar da zaɓen majalisar dokoki a cikin wata mai zuwa.
An kama mutane biyu da ake zargi, amma babu wani bayani game da dalilin da ya sa suka harbe shi.

Asalin hoton, Olayomi Koiki/X
Mai rajin kare ƙabilar Yarbawa a Najeriya, Oloye Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya kai ƙara gaban Firaiminisan Birtaniya, Keir Starmer, domin neman taimakonsa wajen kafa ƙasar Yarabawa.
Mai magana da yawun Sunday Igboho, Olayomi Koiki, shi ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau Lahadi.
Ya ce Igboho ya gabatar da ƙarar ne a madadin jagoran masu fafutukar kafa ƙasar Yarbawa, Farfesa Adebanji Akintoye.
Koiki ya rubuta cewa, "Sunday ya gabatar da ƙarar ne a fadar Downing Street domin ganin ya samun taimakon gwamnatin Birtaniya a fafutukar kafa ƙasar Yarbawa zalla."
Waɗanda suka rufa masa baya lokacin kai ƙarar gaban Firaiministan na Birtaniya sun haɗa da shugaban matasa mazauna waje, Prophet Ologunoluwa, da Ifeladun Apapo da Fatai Ogunribido da sauransu.

Asalin hoton, Social meda
Dakarun tsaron Isra'ila sun lalata wani wuri mai girman gaske a Lebanon, ciki har da wani masallaci mai nisan kilomita 200 daga kan iyaka.
BBC ta samu sahihan bidiyo guda biyu akn lamarin daga yankin Zahajra.
Wani ɗan jaridar Isra'ila ne mai suna Amit Segal da wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum suka fara wallafa hotunan bidiyon.
Sun nuna wasu fashe-fashe guda biyu da suka lalata masallacin Ahel El-Quran , da ke kauyukan Zahajra da Dhayra kan iyakar Isra'ila da Lebanon, da kuma yankuna da ke kusa.
Segal ya yi zargin cewa wurin yana cikin wani ɓangare na Hezbollah kuma suna alaƙa da wani hari da ya janyo mutuwar sojojin Isra'ila biyu shekara ɗaya da ta wuce.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar masu kiwon kaji ta Najeriya ta ce nan ba da jimawa ba kiret ɗin kwai zai iya kai naira 10,000.
Ana dai sayar da kiret ɗaya tsakanin N5,500 zuwa N6,000 a yanzu.
Najeriya na fama da hauhawar farashi mafi muni wanda ba a gani ba cikin shekaru inda farashin kayayyaki ke tashin gwauron zabi a kullu yaumin.
Wasu dai na danganta hakan da tsadar man fetur da kuma ƙarancin kuɗaɗen waje.
Da yake magana a wani taro domin tunawa da ranar kwai ta duniya a Abuja, sakataren ƙungiyar ta PAN a babban birnin tarayya, Musa Hakeem, ya buƙaci gwamnati ta ayyana dokar ta-ɓaci a fannin noman kwai.
Ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ba ta ɗauki matakin gaggawa ba, farashin kwai zai ci gaba da tashi wanda kuma zai ƙara jefa ƴan Najeriya cikin kunci.
Hakeem ya danganta ƙaruwar farashin da tsadar kuɗin sufuri sakamakon cire tallafin man fetur, da kuma hauhawar farashin kayan abinci.
"Hakan zai iya sa farashin kwai ya koma 10,000, duk da cewa yanzu muna sayar da shi a kan 5,500," in ji shi.
Ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan rashin samun tallafi daga gwamnati, inda ya ce an kai sehkara uku rabon da masu kiwon kaji su samu wani tallafi.
Hakeem ya buƙaci cewa a ƙara karfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu kiwon kaji, tare da jaddada cewa ƙungiyar na da dabaru waɗanda za a iya amfani da su wajen magance matsalar.

Asalin hoton, Getty Images
Hezbollah ta ce mayaƙanta na ci gaba da fafatawa da dakarun Isra'ila a wani ƙauye kusa da iyaka da Isra'ila.
Ma'aikatar tsaron Isra'ila (IDF) ta ce ba ya ga sojojinta biyu da aka jikkata, an kwashe wasu da dama da suka ɗan samu raunuka zuwa asibiti.
Faɗa na ci gaba da tsananta a kudancin Lebanon, yayin da jami'ai a can suka ce Isra'ila ta faɗaɗa wajen kai hare-hare a faɗin ƙasar.
IDF ta ce ta kaddamar da hare-hare ta sama kan wurare kusan 200 na Hezbollah a cikin sa'o'i 24 da suka wuce.
A wani lamarin, ƙungiyar agaji ta Red Cross a Lebanon, ta ce jami'anta na sa-kai sun jikkata bayan da wani harin Isra'ila ya faɗa kan ginin da suke gudanar da aikin ceto a kudancin Lebanon.
IDF ɗin ta zargi Hezbollah da amfani da motocin ɗaukar marasa lafiya wajen ɗaukan makamai da kuma zirga-zirga da mayaƙanta, sai dai ba ta bayar da hujja ba kan haka.
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi kira ga Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres da a cire jami'an wanzar da zaman lafiya nan take a kudancin Lebanon.
"Mista Guterres ya kamata ka fitar da dakarun UNIFIL daga shiga haɗari. Yanzu ya kamata, nan take," kamar yadda Netanyahu ya bayyana a wani bidiyo.

Asalin hoton, Reuters
Ƙasashe 40 da ke bayar da gudummawa ga tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya a kudancin Lebanon sun yi kira da a dakatar da hare-haren da ake kai masu cikin gaggawa.
Wata Sanarwa ta haɗin gwiwa da suka fitar, ta ce rawar da rundunar ta UNIFIL ke taka wa na da matukar muhimmanci idan aka yi la'akari da yadda lamarin ke ƙara ta'azzara, yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai farmaki kan ƙungiyar Hezbollah.
Dakarun wanzar da zaman lafiya biyar ne aka raunata cikin ƴan kwanakin nan kuma Isra'ila ce ta yi sanadin huɗu daga cikinsu.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu da ake zargin ƴan bindiga sun toshe babbar hanyar Gusau zuwa Funtua mai cike da cunkoso tare da yin awon gaba da matafiya da dama.
Ƴan bindigar sun tare babbar hanyar da ke tsakanin al’ummar Kucheri da Magazu a karamar hukumar Tsafe, inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi.
Mai magana da yawun ƴansandan jihar ta Zamfara, ASP Yazid Abubakar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels, ya ce an yi garkuwa da mutanen da ba a tantance adadinsu ba a harin.
Ya ce jami’an tsaro na can suna hoɓɓasa don ganin an ceto mutanen da aka tafi da su.
“Lamarin ya faru ne da yammacin jiya Asabar. Ƴan bindigar sun tare hanya suka fara harbin kan masu tafiya inda suka yi garkuwa da wasu daga cikinsu,” inji kakakin ƴansandan.
Ya ce jami'ansu tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro suna aiki tare don ganin an ceto waɗanda aka sace.
Sai dai Abubakar ya musanta rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da ‘yansanda biyar a lokacin da suke artabu da ‘yan bindigar.
Zamfara dai na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren gungun 'yan bindiga, waɗanda ke yin garkuwa da jama'a domin neman kuɗin fansa.

Asalin hoton, Lebanese Red Cross
Ƙungiyar agaji ta Red Cross a ƙasar Lebanon ta ce an aike da tawagogin motocin ɗaukar marasa lafiya zuwa Sirbine da ke kudancin Lebanon, bayan wani hari ta sama da aka a safiyar yau.
Ta ce an ɗan jikkata masu aikin sa-kai a wajen aikin ceto - lokacin da aka kai hari karo na biyu a yankin.
"Ya kamata a kare masu sa-kai na Red Cross a Lebanon a kowane lokaci yayin da suke ƙoƙarin ceto waɗanda suka jikkata," kamar yadda sanarwar da ƙungiyar ta fitar ta bayyana.
Sojojin Isra'ila sun umarci Falasɗinawan da ke zaune a arewacin Gaza da su fice daga yankin.
Sai dai babu adadin mutanen da suka bar yankin kawo yanzu.
Hotuna da dama sun nuna yadda mutane ke ta tserewa yankin daga jiya Asabar.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, X/Multiple
Yar takarar shugaban ƙasar Amurka a Jami'yyar Democrat, Kamala Harris ta kalubalanci abokin hamayyarta Donald Trump na Jam'iyyar Republican da ya tabbatar da cewa yana da ƙoshin lafiyar da zai iya tafiyar da aikin ofishin shugaban ƙasa.
Harris na magana ne bayan fadar White House ta fitar da wata takarda daga likitanta wanda ke nuna cewa tana cikin koshin lafiya.
A nasa ɓangaren a wani gangamin da ya yi a California, Mista Trump ya sake zaƙe wa kan batun ƴan ci-rani, inda ya zargi ‘yan jam’iyyar Democrat da shigo da abin da ya kira “Rundunar masu aikata laifuka a ƙasar.
Trump ya ce duk wanda zai shigo da gungun masu aikata laifuka domin su mamaye Amurka bai cancanci ya yi takarar shugabancin ƙasar ba.

Asalin hoton, EPA
Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce aƙalla mutane 15 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama a sassa daban-daban na ƙasar.
Ɗaya daga cikin wuraren da aka kai wa hari shi ne Deir Billa da ke arewacin ƙasar Lebanon, wanda wannan ne harin farko da aka kai yankin.
Rundunar IDF ta ce mayakan Hezbollah sun harba rokoki sama da 300 zuwa cikin Isra'ila a ranar Asabar, inda ta kuma umurci mutanen da ke zaune a kudancin Lebanon da su fice daga yankin.