Neymar zai ci gaba da wasa a Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Neymar zai ci gaba da taka-leda a Barcelona duk da rade-radin da ake cewar zai koma Paris St Germain a bana.
Mataimakin shugaban Barcelona, Jordi Mestre ne ya tabbatar da cewar ba za su sayar da dan kwallon ba, zai kuma buga kakar wasan da za a fara a Spaniya.
Rahotanni a Spaniya sun ce PSG na son sayen Neymar mai shekara 25, bayan da kungiyar ta dauki abokin wasansa a tawagar kwallon Brazil, Dani Alves.
PSG ta dauki Alves tsohon dan wasan Barcelona da Juventus, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a kakar da ta kare.
Neymar ya koma Barcelona a 2013, a kuma watan Oktoban 2016 ya tsawaita zamansa a Camp Nou kan yarjejeniyar shekara biyar.








